Ni fa zuciyata tuni ta gama nutsuwa da cewa wani sashe daga cikin mutane irin su Masu Daraja Socrates, da Alexander the Great (Zul-Qarnanain), daSamuel (Shamawilu), da Aristotle, da Gautama Buddha, da dai sauran ire-irensu (amincin Allah ya tabbata a garesu), wasunsu annabawa ne da mursalai, wasunsu kuma manya-manyan waliyyan Ubangiji ne. Don haka, idan ana maganar me magabata suka ce akan rayuwa, ko mai suka fahimta, to matuqar ba ta Khatimun Nabee’ina (SAW) bace, ko kuma ta sahabbansa (Radiyallahu Anhum), to tabbas wata gabatar ta fi wata.


Idan kuma ana maganar wadannan manya-manyan salihan bayanin Allah din da suka rayu dubban shekaru da suka shude ba wai daruruwa ba, kuma gasu masana, kuma masu yin tunani, ga kuma ilhama, to kada wani ya kuskura ya yi mana managar wani Uthaimin ko Dan Taimiyya ko Abdulwahab, ko ma wani mutum can da ya rayu daruruwan shekaru bayan wafatin Manzon Allah. Tabbas magabatan naku su ma sunyi qoqari qwarai, amma fa irin na zamaninsu da kuma amfani da bayanan da ke ‘available’ a zamanin nasu, amma fa ina da tabbacin mutanen zamaninmu sun fi magabatan naku ilimin duniya da fahimtar rayuwa, kuma hakan ta samu ne saboda tunani da muka runguma a zamaninmu kamar yadda su Socrates (Alaihis Salam) suka koyar, ga kuma uwa-uba ILIMIN FASAHA da Allah ya azurta wannan zamaninmu dashi.


Kai ni wallahi ina ma matuqar tsoron matuqar tun yau ba’a dauki matakan akan a saisaita zukatan al’umma daga tsatstsauran ra’ayin riqau irin nasu Uthaimin da su Abdulwahab ba, to kuwa ba abin mamaki bane idan akace wani zamani zai iya zuwa anan gaba da wani rukunin mutanen zasu ke bada tarihin irin gwagwarmar da wani masani kuma babban mujahidi da akayi a Ifriqiyya Sudaniyya wanda yasha gwagwarmaya da gwamnatocin qasahen dagutai har guda hudu a lokaci guda, wato Sheikhul Islam Abu-Muhammad Abu-Bakr Ash-Shekawiy (Radhiyallahu Anhum).


To ya kenan ya kuke tunanin duniya zata kasance idan ire-iren fatawowinsa suka zama ruwan dare a duniyar musulunci a wancan zamani mai zuwa?


Wassalamu aleikum,


A sha tunani lafiya.

Las Danbuzu

Facebook Comments

Leave a comment

Copyright (c) 2020 danbuzu.com

Minimum 4 characters