Da farko dai ita wannan duniyar tamu gaba ɗayanta ma ba wani daɗewa tayi da samuwa ba idan muka kwatanta lokacin samuwarta da kuma lokacin samuwar shi ainihin sararin samaniyar da komai ke cikinsa. Shi dai sararin samaniya, ko kuma nace sararin subuhana, ya kai shekaru biliyan goma sha uku da miliyan ɗari takwas (13.8 billion years) da samuwa, kuma ya samu ne daga babu sakamakon wata babbar ƙara/tsawa da ta faru (Big Bang) kwatankwacin irin ƙarar banger ɗin nan da yara ke bukukuwan sallah da Kirsimeti dasu, a waɗannan shekarun da na ambata, sai kuma sararin samaniyar yaci gaba da faɗaɗa. Nan gaba kuma ana sa rai idan ya kai ƙololuwar faɗinsa zai koma ya fara tsukewa har sai ya koma Asalinsa na babu (Big Crunch). A ɓangare ɗaya, ita kuma duniyar nan tamu ta Earth (أرض) a yanzu shekarunta biliyan huɗu da miliyan ɗari biyar da arba’in da uku (4.543 billion years) kacal da samuwa. Kuma wani abu da zai bayar da sha’awa ciki lamarin Ubangiji, shine, ita wannan duniyar da ma sauran duniyoyin (Planets – كواكب) da ke kewaye da rana, duka sun samu ne daga tarkacen da suka rage (Leftover) na daga samuwar rana (Sun – سمش), kuma duka gabakin ɗaya duniyoyin tara da kake gani tare da watannin wasu daga cikinsu duka sun samu ne cikin shekaru miliyan ɗari (100 million years) kacal bayan samuwar rana wacce ita kuma ta kasance ɗaya daga cikin taurari (stars – نجوم) ce dake tsugunne a unguwar taurari (Galaxy) ta Milkyway ne.

A cikin kowanne Galaxy akwai biliyoyin taurari ba adadi, manyansu da ƙananunsu, wadda Ita kanta tauraruwar mu, wato rana (Sun – شمس) idan ka ɗauke ta ka je fata kan wata tauraruwar, to misalin yin hakan bai wuce ace ka ɗauki hancin bironka ka jefoshi cikin duniyarmu daga wajenta ba. Kuma su kansu galaxies ɗin suna wanzuwa ne a rukuni-rukuni da ake kira da suna Clusters a cikin sararin samaniya (Universe), wanda su ma clusters din Allah he kadai ya san adadinsu. Su taurari sun kasance wasu na mutuwa ne wasu kuma na samuwa. Kai in taƙaice maku zance ma, acikin taurarin da muke gani da idan mun ɗaga kanmu sama da dare kullum, akwai waɗanda tuni sun mace sun rigayemu gidan gaskiya, haskensu da ya baro su ya taho garemu bai iso mana ba tun suna raye ba sai bayan sun mace da daɗewa saboda tsabagen nisan da ke tsakaninsu da mu, da kuma matuƙar fadin da sararin samaniya take dashi.

A halin yanzu ma maganar da ake yi itace ita kanta sama (universe) ɗin ba guda ɗaya bace. Kai ana ma sa ran ko a nan sararin da muke wanzuwa ma akwai wasu sammai ɗin marasa adadi suma a cikinsa amma sai dai kowaccensu tana wanzuwa ne a ‘dimension’ na daban da namu, da kuma ɗabi’a da dokoki daban su ma da namu. Kuma ana ma sa rai cewa duk abinda ya faɗa cikin ‘Black Hole’ to wata saman yake faɗawa.

2.
Shi kuma wannan wata (Moon) namu da muke ƙidaya da lissafin shekaru da shi (Lunar Callender) Yana daga cikin jerin tsararrun shirgin da ake kira da turanci ‘Satellites’ da ke cikin sararin samaniya suna zagaya duniyoyin su. A farkon samuwarsa, wata ya kasance yana da ɗan’uwa, ma’ana su biyu ne suka samu, sai dai ɗaya ya kasance babban ɗaya kuma ƙarami. Kuma su duka sun samu ne sakamakon ɓantarewa da duniya tayi a sabili da taho-mu-gama (collision) da aka samu tsakanin duniyarmu a lokacin bata ma gama haɗuwa ba da kuma wani murgujejen dutse wanda girmansa ya kai kwatankwacin girman duniyar ‘Mars’, wanda aka kira da suna ‘Theia’, wanda shima yana ɗaya daga cikin tarkacen da suka rage na daga samuwar rana. Sai dai duk a cikin shekaru miliyan ɗarin nan na farko bayan samuwar rana, su waɗannan tagwayen watannin namu guda biyu dake zagaya duniyarmu cikin tsananin hanzari, su ma sun yi gaba da gaba da juna, shi dai babban ya tsira, amma shi ƙaramin ya tarwatse ya zama wata irin ƙura da ta ci gaba da wanzuwa kewaye da babban, sannan daga bisani an ɗauki lokaci mai tsawo ana luguden duwatsu ba ƙaƙƙautawa akan shi babban watan da ya tsira. Hakan tasa duk wanda ya sauka akan doron wata, ɗaya daga abinda yake fara yin kaciɓis dashi bai wuce tarin ‘Craters’ marasa adadi ba wanda sun samu sakamakon tarin raunin da ya samu daga luguden duwatsu, duk da dai shi watan ya samu ya mulmular da kansa izuwa mumulallen farin wata da muke gani a yanzu. Mu kuma a nan duniya ana sa rai watan ya bantare ne daga daidai inda tekun nan mafi girma da zurfi take wanzuwa a halin yanzu, wato tekun PACIFIC.

3.
Yanzu kuma sai maganar samuwar ruwa da halittu masu rai a banƙasa kafin mu zo ga samuwarmu mu jinsin bil’adama. Ko shakka babu sai da ruwa ya samu sannan rai ta biyo baya. Sannan yazuwa yanzu bayanan da ake dasu sun nuna cewa rai ta farko a cikin wannan duniyar tamu ta kasance wata nau’in Bacteria ce da ake kira da suna CYANOBACTERIA.

Kash! Wallahi na gaji! A gafarce ni, amma zan ci gaba.

Leave a comment

Copyright (c) 2019 danbuzu.com