Mutanen duniya sun kasu gida biyu:

1. Wadanda suka gasgata kasantuwar Ubangiji.
2. Wadanda suka qaryata kasantuwar Ubangiji.

Masu gasgata kasantuwar Ubangiji ma su kansu su ma sun kasu gida biyu:

1. Masu da’awar Ubangiji qwaya daya ne tal.
2. Masu da’awar akwai Ubanningiji fiye da guda

Alal misali: A cikin addinin Hindu akwai alloli maza da mata marasa adadi, kuma akan sami allah ya auri alliyah fiye da guda. Kai an ma sami alloli na gaba da juna akan mace (alliyah), inda har ma an sassami fadace-fadace da gaba da juna a tsakanin allolin.

Bari dai na taqaita surutu na taho kan addinin Islama kai-tasaye!

Mafi akasarin al’ummar Musulmai a duniyarmu ta yau, zaka samesu ko dai akan mazahabar Sunnah ko kuma akan ta Shi’a, wadanda su ne manyan rassan addinin Musulunci guda biyu da ake dasu, kuma suke gaba da juna, alhali sabanin siyasa ne ya haifar a bayan wafatin Manzon Allah (SAW), wanda kuma daga bisani rukunnan ibada da dama suka banbantu a tsakaninsu, bayan da aka rurrubuta littafan da a cikinsu an caccakuda qarya da gaskiya domin danne abokin hamayya daga kowanne bangare. Bugu-da-qari, kowannensu yana ga shine akan daidai, shi kuma abokin gabarsa akan tafarkin bata. Kuma ma kowa na kallon cewa yadda shi yake gudanar da addininsa shi ne daidai, ba yadda abokin hamayyar tasa ke yi ba.

Sannan kusan duka hujjojin da bangarorin biyu ke tnqaho dasu, suna cikin littafan tarihi ne da kuma wasu daga cikin hadisai. Kuma wallahi tallahi akwai qarerayi marasa qidayuwa a littafan tarihi. Misali: Da Danfodiyo bai yi nasara a jihadinsa ba, da yanzu muna lissafashi a cikin manyan ‘yan ta’addar da aka taba yi a Afirka. Hakazalika, da Sheqau yayi nasara, da yanzu an fara wallafa littafai akan falalolinsa da karamominsa.

Idan kuma muka koma kan hadisai kuwa, zaka fahimci cewa daya daga cikin guraren da aka ja layi tsakani Sunnah da Shi’a shine jerin Littafan Hadisai daban-daban da kowa ke amfani da. Kuma malamai da yawa sun yi ittifaqin an qirqiri hadisai marasa qidayuwa domin nuna falalar wani ko qasqantar da wani a tsakanin bangarorin biyu masu gaba da juna.

Baya ga wannan gabar da ke tsakanin Sunni da Shi’i, kana gangarowa cikin su kansu Sunni din masu karanta Buhari da Muslim da Turmudhi, su ma akwai gaba tsakanin sassansu.

Bari in dan bada misali da abinda muke gani a Nijeriya:

1. Salafawa (Wahabiyawa) suna yiwa Sufaye (‘yan Dariqa) kallon Mushirikai duk da cewa su duka Sunni ne.

2. Su kansu Sufaye an sha sassamun gwabzawa da zubar da jini tsakanin bangororinsu mabanta, wato, ‘yan Qadiriyya da ‘yan Tijjaniyya. Mun ma sha jin Qadirawa na rera waqoqi suna cewa “Dan qabalu (Tijjaniyya) kurege ne, in ya mutu a kai bola”.

3. Haka-zalika su kansu Salafawa din sun sha yin artabu a tsakaninsu har ta kai ga wani bangaren baya bin wani bangare sallah.

[ Izala Bush vs Izala Saddam]
Izala Jos vs Izala Kaduna]

Kai daga qarshe ma sai wasu rukuni da suka kira kansu ‘yan baruwanmu a rikicin suka ware suka kira kansu ‘Yan Salafiyya, suka kafa wata majalisa mai suna ‘Ta’awun’ a Kano, a shekarun baya ma na ji labarin cewa an kori Sheikh Ibrahim Khalil daga cikin ta saboda wasu matsayoyinsa da ya saba da nasu.

Abin tambaya anan shi ne: Wai wane ne yake a kan daidai?

Tun daga kan masu akwai Ubangiji ko ba Ubangiji, masu Musulunci ko akasinsa, zuwa kan ‘yan Sunnah ko Shi’a. Wane ne ya taba zuwa lahira ya gano cewa tabbas shi ne akan daidai?

Shi fa addini ko akasinsa magana ce kawai ta imani. Duk fahimtar da wani ke kai, kuma yayi imani da ita, to a fahimtarsa ita ce daidai. Kuma mafi akasarin mutane sukan yi imani da abinda suka taso suka taras da iyayensu da kakanninsu akai ne.

Ni dai shawarata daga qarshe ita ce:

Abinda yafi komai muhimmanci dai shine mu mutunta junanmu, kuma mu tuna cewa dukkanin mu ‘yan’Adam ne. A kuma bar kowa ya rayu akan fahimtarsa da abinda yayi imani dashi. Idan kuma har kana yiwa dan’uwanka sha’awar yazo yabi tafarkin da ka kasance kana akai, to ka kirashi cikin hikima da mutuntawa. Amma daga lokacin da ka nuna ma mutum baka qaunarsa saboda abinda yayi imani dashi, to kamar ka qara masa qawarin gwiywa ne akan ya qara jajircewa akan hakan.

Tabbas da Allah ya so da ya yi mu gabakidaya jinsi daya, qabila daya, addini daya, al’umma daya. Amma sai yayo mu a haka saboda da hakan yake so ya ganmu, kuma tabbas yana so hakan ya zama darasi ga masu hankalin cikinmu.

Kada mu manta cewa a cikin mutane sama da mutum 7,800,000,000 da muke da su a fadin duniya, kusan mutum 1,800,000,000 kadai ne musulmai, sauran sama da mutum 6,000,000,000 din da sun ma haura 75% na al’ummar duniya ba Musulmai bane. Idan kuma aka qara cire wadanda ba ‘yan qungiyarka ko mazahabarka ba daga jerin Musulmin duniya, to a lissafe ka qara yiwa addinin dake kake ta talla azo a shiga gibi kai da kashin kanka.

Idan kuma ku da kuka rage din kuka yi qoqarin gallazawa wani da ba dan naku ba, to ku tuna, sarkin yawa fa yafi sarkin karfi. Kuma daman ina ma qarfin yake?

Kasashen Musulmai ma nawa ne ke da makamin Nukiliya?

Wacce qasar Musulmai ce ake lissafa ta a jerin qasashen da suka ci gaba a duniya?

Wacce ce ke da qarfin fada a ji afadin duniya?

Qasar Saudiyya kadai ma ta isa misali.

Allah dai kawai yasa mu cika da imani., Amin.

Danbouzu LAS
Twitter/Instagram/YouTube – @danbouzu

Facebook Comments

Leave a comment

Copyright (c) 2020 danbuzu.com

Minimum 4 characters