A kundin tsarin mulkin Qasarmu Nijeriya ba wani mahalukin da ya isa ya haramta Mazahabar Ja'fariyya (Shi'anci), kamar yadda ba wanda ya isa ya haramta tafarkai irinsu Wahabiyanci da Sufanci. Amma dai, idan gwamnati taso, tana da damar ta soke 'register' da ta baiwa kowacce irin qungiya cikin harda qungiyoyin addinai irin su NASFAT, Izala, Islamic Movement of Nigeria (IMN) da sauransu, matuqar buqatar hakan ta taso.

A kwanakin baya wata kotun Nijeriya ta haramta qungiyar IMN, amma kuma ita koyarwar Shi'anci tana nan daram dam zaune da gindinta kamar yadda koyarwar Wahabiyanci da Sufanci da sauransu ke nan, hasali ma, sake sunan qungiya kawai 'yan Shi'a zasu yi su ci gaba da gashi, tunda suya ai sai ranar sallah.

A tunanina, muddin gwamnati na muradin ta mangace ayyukan 'yan qungiyoyi masu tada zaune tsaye ko raba kawunan al'umma, to daya daga hanyoyin ita ce, sai ita gwamnatin ta haramta dukkannin wata qungiyar addinin gaba daya face Jama'atu Nasril Islam (JNI) da Christian Association of Nigeria (CAN) a Nijeriya. Misali: A Wahabiyanci kadai akwai qungiyon raba kan al'umma guda uku:-

Izala (Jos),
Izala (Kaduna),
da kuma Salafiyya mai cibiya a Kano

Haka-zalika akwai a Quadiriyya.
Haka-zalika ma a Tijjaniyya,

ga dai su nan birjik ba adadi.

Wanda kuma a lokuta da dama zaka samesu ba sa ga miciji ga junansu.

A cikin koyarwar Sufanci kuwa, a shekarun baya an sha samun qazaman fitintunu tsakanin Tijjaniyya da Quadiriyya; a Wahabiyanci ma an sassami fitintinu marasa dadin ji tsakanin Izala Bush da Izala Saddam. Ga kuma rikicin kwana-kwanan na rikicin shugabanci da kason kudi a cikin Quadiriyya, wanda ita ma ka kekkece.

To amma da gwamnati zata rushe dukkan qungiyoyin addinai din ta bar JNI da CAN kacal, da wallahi ya fi mana alheri, kuma da an sami sauqin rabe-rabe da qyamar juna a tsakani al'umma, ko kuma ma nace a tsakanin su kansu al'ummar Musulman.

allah dai kawai yasa mu dace

Wallahu a'lam.

Las DanbuzuFacebook Comments

Leave a comment

Copyright (c) 2020 danbuzu.com

Minimum 4 characters