1. Kasancewar an sanyawa kalma suna ta أرض mu’arifah (ال)، to kai tsaye mun san anan Allah yana magana da mala’ikunsa ne akan duniyarmu (Earth) a cikin wannan aya mai lamba ta 30, a cikin Suratul Baqarah.

2. Abin tanbayar anan shine: Shin ta yaya ma mala’iku suka san bil’Adama zasu ke zubar da jini a ban qasa? Shin Allah ne ya sanar dasu halayenmu ko kuma dai kawai ya kimsa masu sanin hakan ne?

3. Ko kuma ma wasu ne suka rayu kafin mu a duniyar, kuma suka zuzzubar da jinin juna? Shin idan kuma wasu masu kama damu ne suka rayu har suka ja mana irin wannan shaidar to su din su wane ne? Kuma mene ne jinsinsu?

4. Akwai maganganu da yawa akan su wane ne suka rayu a duniya kafin Allah ya halicci Annabi Adam (AS). Mafi yawan mutane sun fi raja’a akan cewa ai wani jinsi ne na aljannu suka zauni duniya a baya. Sai dai kuma akwai maganganu masu yawa da suka nuna cewa wasu mutanen ma sun rayu kafin halittar kakanmu Annabi Adamu. Bari na kawo wani misalin guda:

An ruwaito daga cikin littafin ‘Ain ul Faqr (a cikin peji na 285), wanda yake littafi ne na wani babban Malamin Islama, kuma mabiyin Dariqar Qadiriyya Wanda ya rayu a qarni na 17, cewa, “Allah ya taba gayawa manzonsa cewa: ‘Ya kai Muhammad, na halicci wani Adam din kafin na halicci kakanka Adam, wanda na hore masa rayuwar shekara 1,000, sannan kuma sai na halicci wasu Adamu-Adamu din guda 15,000, wadanda su kuma na hore masu rayuwar shekaru 10,000. Sannan kuma daga bisani sai na halicci Adamu kakanka.

Allah yayi mana mai kyau!

To zamu iya tattaunawa?

Facebook Comments

Leave a comment

Copyright (c) 2020 danbuzu.com

Minimum 4 characters