Ba wai wani qwaqqwaran binciken na gabatar ba, amma ina da niyyar gudanar da shi qwaqqwaran binciken. Amma kafin na afkawa shi binciken, akwai abubuwan da na ke zato dangane da shi Madiqo a qasar Hausa din. Wanda shi binciken nawa da zan yi, zai zama ko dai ya gasgata ko kuma ya qaryata wadannan matsayoyi nawa wadannan na cimma a sakamakon dan gajeren nazari da kuma tattara bayai da nayi tunda fari.

Ga wasu daga cikinsu:

1. Madiqo ya fi zama ruwan dare a tsakanin ‘yan Arewa Musulmai idan aka kwatantasu da ‘yan kudu kamar yadda muka taba tattaunawa da Muslimu Khamis. Kuma hakan ba zai rasa nasaba da yadda al’adarmu ke qoqarin nisanta mu’amala tsakanin jinsin maza da mata ba domin gudun lalacewa kamar yadda ake fadi, sai su kuma matan ‘curiosity’ yake sanya su suna kwatanta yin abinda ake gudun kada suyi da jinsin maza a yayin cudanya. Wanda kuma daga qarshe sai su zama addicted da hakan.

2. Ba kasafai ake sanyawa dangantaka ko kebanta taskanin mace da mace ba idanu ba, wai saboda ai jinsinsu daya. Kenan kamar al’ummarmu ta fi maida hankali wajen kyamatar dangantaka tsakanin mabanbantan jinsi.

3. Madiqo ya fi zama ruwan dare a tsakanin matan da suke da galihu ko kuma suka fito data gidan akwai.

4. Akwai tarin matan aure da suke aikata madigo, kuma kaso mai tsoka daga cikinsu irin matan nan ne da aiki ko tafiye-tafiye suka yiwa mazajensu yawa.

5. Tabbas ya bayyana a gareni cewa Birninmu na Katsina na daya daga cikin biranen Nijeriya dake da tarin mata ‘yan madigo.

NB:
Lallai comments dinku na da matuqar muhimmanci a gare ni da kuma wannan bincike nawa, domin zan yi amfani dasu a binciken. Abinda nake so daku kawai shine: Ga duk wani ko wata dake da qarin bayani to ina da buqata. Kuma idan akwai gyara a matsayata don Allah a gyara mani. Tabbas zan fi maida hankali da yin amfani da mafi rinjayen ra’ayi da fahimta, sannan daga qarshe nazo da mafita.

Don Allah banda son rai!

Na gode.

Signed:
Danbouzu LAS
(Twitter/Instagram/YouTube – @danbouzu)

Facebook Comments

Leave a comment

Copyright (c) 2020 danbuzu.com

Minimum 4 characters