Wato abubuwan da zasu baka haushi dangane da Malam Bahaushe basu ba za su taba lissafuwa ba saboda tsabagen yawansu. Domin kuwa adadinsu ma ya tasamma adadin shura qafar masaqi. Amma dai bari na dan lissafo qwaya biyu daga ciki, kafin daga bisani na ci gaba wata ranar:

  1. Da farko dai shi Bahaushe yana ganin duk mutumin da ke tsakiyar Hausawa, sai kuma akayi rashin sa’a sunansa ba na larabci bane, to wai ba cikakken musulmi bane, kuma ko da kuwa gadar musuluncin yayi a wajen iyayensa, ballantana kuma ace kutse yayiwa addinin. Misali: Idan sunanka Obinna ko Simon, sai kuma ka gabatar da kanka a matsayin musulmi, to yasin ka higa ukku a wajen Hausawa, domin kuwa dole sai sun tafka muhawara akanka, cewa ko dai kutse kayowa addinin ko kuma ma kai ba musulmi nagari bane. Idan kuma kazo masu da Bahaushen suna tantagaryarsa, to yasin sai wasunsu sun yi zargin anya kai ba bamaguje bane ba kuwa. Hakan tasa Hausawa ke ta zubar da sunayensu da al’adunsu suna rungumar na larabawa, domin su wai a zatonsu da larabci da musulunci duk abu guda ne. Idan kuma da ace wata mai suna ‘Happiness’ zata zo ta karbi musulunci, to tabbas sai sun tambayeta sunan larabcin da take so a sauya mata nata da, ko da kuwa ma’anarsa guda da natan, wato ‘Farhanatu’, ma’ana dai ‘Farin Ciki’. Kai idan ma tayi rashin sa’a, zasu iya rada mata Lantana, Akhrajna Ko wata Kalmar larabcin ta daban, musanman idan daga Kur’ani aka cirota, kuma ko da magana ce akan narkon azaba. Wallahi tallahi ni nan da kaina na taba gamuwa da wata yarinya mai suna Harijah. Allah dai kawai ya kyauta.Da ace Paul Pogba, Fredrick Kanoute, Riberry, Eden Dzeko, Kolo Toure, da sauransu, da sun higa tara. Na rantse da Allah na yiyyi mu’amala da mutane masu snayen Muhammadu da Ahmadu kuma kiristoci ne, wai ban da ma sauran sunayen larabci kenan. Sakarcin banza kawai.
  2. Na biyu, mafiya yawan Hausawa suna yin Musulunci ne kawai a matsayin addinin gado, saboda kadai an haihosu a cikinsa. Da kuma za’a samu wani wanda yayi ta maza ya baro wani sashe na iyayensa da ke yin wani addinin ya taho ya rungumi musulunci, to da sai Hausawa sun dinga yi masa gorin wai ai uwayensa ko wani sashensu ba musulmi bane, wanda kuma a zahiri shi din ya fi su zama zakaran gwajin dafi a musuluncin, saboda ai shi yarda yayi da addinin ya shigo ba wai gadarsa yayi kamar su ba. Kai in ma taqaice maku zance: Shi fa Bahaushe gani yake daga Balarabe sai shi a addini, kai idan ma tayi wani juyin sai Bahaushe yace maka ai shi ya ma fi Balarabe yin Musuluncin. Idan Kuma da wani daga wata qabilar shi ma zai zo wajen Bahaushe, kuma ko da ya kai alhuda-huda ilmin addini, ga kuma ibadah da sallah kamar sallau, to yasin Bahaushe na iya cewa a rabu da musuluncin qabila kaza.

Hmn… Kawai da abinda zan ce shi ne ‘Allah ya shiryi Malam Bahaushe’.

Facebook Comments

Leave a comment

Copyright (c) 2020 danbuzu.com

Minimum 4 characters