Bubaddiyar Wasika zuwa ga Gidan talabijin na Dadin Kowa StarTimes: ‘Wa ya baku Sadauki?’


Hakika Gidan talabijin na Dadin Kowa StarTimes su aikata babban zunubi ga kamfanin shirya fina-finai na Giggs International.

Tsakani da Allah, wane ne ya baku damar kuke yin amfani da suna tare pastocin film din Sadauki kuna tallata tasharku ba tare da kun nemi iznin kampanin dake da hakkin mallakarsu ba?!

Bari na dan yo tariyar baya:

A da, idan kampanin shirya fina-finai na so ya sayarwa wani gidan talabijin film din da ya shirya, sai kaga gidan talabijin din na ta yauki yana yanga tamkar farar mace a Kano. Kuma hakan bai rasa nasaba da rashin ingancin fina-finan da ake shiryawa a masana’antar Kannywood din. Kuma tabbas haka abin yake, saboda wallahi wani lokacin idan kana kallon wani film din a wata tashar talabijin din, idan aka nuna wata rashin iyawar da rashin kwarewar, sai kaji kamar kace ‘Allah ya isa kudin subscription dina’. Kai wani lokacin ma sai kaga har kana yarda remote a kasa saboda hanzari da kakeyi wajen sauya tashar saboda rai da suka bata maka.

A baya idan zamu iya tuna wani namijin kokari da babban mashiryin fina-finan na, kuma babban mai bada umarni, wato Hassan Giggs yayi, to tabbas ba zamu gushe ba har sai mun daukeshi a matsayin zakaran gwajin dafi a masana’antar ta Kannywood. Hassan Giggs yayi kokari matuka wajen sauya akalar kampaninsa mai suna Giggs International daga kan gwadaben da Kannywood ta dade akai shekara da shekaru, da zummar ganin ya kawo wani sabon salo, sabanin wanda aka saba da shi tun fil’azal. Misali:

-Dan yawan masu daukar nauyin film a Kannywood basu so su zuba kudi masu yawa su shirya film mai ingancin, duk da kuwa sun san da cewa duk abu mai ingaci baya kwantai.

-Suna gudun labari mai zubin zamanin da, saboda zai bukaci mutane masu yawa da kuma tarkace irin na wannan zamanin. Kuma hakan zai bukaci kudi masu yawa.

-Kuma ko a ire-iren labarun da suke so, masu shirya fina-finan kan sauyawa marubuta salon labarinsu saboda a gujewa anfani da wani abu da ka iya kara sanyawa a kashe kudi. Hakan tasa da yawa daga labarun da ake shiryawa fina-finai basu wuce ace,

Saurayi ya yaudari budurwa,

‘Yar mai kudi ta makalewa talaka,

Amarya tayiwa uwargida asiri,

Uba ya gamu da ‘yarsa a wajen bariki,

Da dai sauran ire-iren wandannan.

Bahaushe yace arha bata ado, saboda haka Hassan Giggs ya lashi takobin shirya fina-finai masu dauke da yanayin zamanin da, wandanda duk da cewa ya san zasu lankwame miliyoyin Nairori, amma tabbas yana da yakinin zasu kawo babbar riba a bisa doron salon maganar nan da Hausawa ke cewa ‘da taron yuyuyu gwara d’a daya kwakwara’.

Sanin duk wani mai bibiyar abinda ke faruwa a Kannywood ne, a karshen Shekara ta 2018, Hassan Giggs ya saki wasu fina-finai masu suna ‘Sarauniya’ da ‘Wani Karni a sinima’. Wanda kuma zunzurutun kwarewa da iyawa da aka nuna a fina-finan ya kawo masu farin jini/matuka-gaya, haka har tasa aka dinga gayyatar kampanin zuwa gidaje da ofisosi yana haska film din a wani salo da ake kira da ‘VIP Show’, wanda kai da iyalanka ko abokan aikinka zaku gayyato Kampanin Giggs international din da yazo har inda kuke ya haska maku film din, ba sai kun je sinima ba. Wannan kuwa shine irinsa na farko a Kannywood.

Dangane da film din Sadauki kuwa, film din na daya daga cikin mafarkin Hassan Giggs wajen ganin an sake zana manhajar shirye-shiryen Kannywood. Film din an shirya shi ne a cikin shekar 2018, da nufin a rikita sinimun Nijeriya, kai har ma da wasunna tsallake a cikin wannan sabuwar shekarar ta 2019. Amma sai kwatsam wani abu wanda bai taba faruwa ba ya faru:

A da, masu shiya film ne ke biyan kudi da a tallata masu fina-finansu a kafafen sadarwa, ko kuma suke godon a sayi film din su a ‘yan kudin da basu taka kara sun karya ba domin haskawa a gidan talabijin. Amma a wannan karon, sai ga wani gidan talabijin an kama dumu-dumu da satar fasaha daga wannan kampani na Giggs International dake masana’antar ta Kannywood.

Kasancewar Film din Sadauki, film ne da ya kunshi wani salon wanda ba kasafai furodusoshi da daraktocin ke iya jura ba. Misali:

An yi amfani da mutane ba adadi,

film ne da ke kunshe da saddabaru iri-iri,

film ne wanda aka tsaya aka shiryashi tsakani da Allah ba ganda, ba kwauro,

kuma hakan tasa film din ya riga da tuni yayi shuhura tun ma kafin mu shigo shekarar 2019 din.

Shi kuma gidan talabijin na Dadin Kowa StarTimes, sai yayi amfani da wannan damar ya dauko poster da sunan Sadauki ya tallata kansa saboda yayi imani Film din ya fi gidan talabijin din shuhura, saidai kash! Ya yi hakan ne ba tare da ya nemi amincewar kampanin Giggs International din ba. Soboda haka, wannan babban laifi na satar fasaha ya haifar da ‘ya’yan laifuka kamar haka:

-An saci suna da poster Sadauki anyi tallan gindan talabijin din ba tare da izini ba.

-An yi kokarin zubarwa kampanin Giggs International mutunci a bainar jama’a ta sigar yiwa mutane karya da sunan za’a ke haska film dinsu rana kaza da rana kaza, kuma a ci gaba a rana kaza da rana kaza. Wanda a zahirin gaskiya bamu ma san me aka nunawa makallata tashar ba a wadannan ranakun da sunan Sadauki. Wanda tabbas hakan ya kasance yunkurin yiwa Sadauki zagon kasa.

-Kuma an yaudari al’umma ta sigar da zasu iya yin tunanin an hada kai ne da kampanin Giggs International an ce masu za’a ke nuna Sadauki a tashar, sai bayan mutane sun yi tururuwar sayen recorder da yin subscription domin su kalli Sadauki, sai kuma suka ga ashe yaudara ce.

Daga karshe, kampanin Giggs International na mai sanar da jama’a musamman masu sha’awar kallon fina-finanmu da cewa:

Ya zuwa yanzu babu wani gidan talabijin ko wani dan kasuwa da ya mallaki hakkin mallakar Sadauki, saboda haka, duk mai son kallon Sadauki, to kadai za’a iya kallonsa ne a sinimu da wuraren da aka ware domin kallonsa a birane daban-daban a lokuta mabanbanta.

Kuma duk garin da za’a shigo domin haska Sadauki, za’a sanar a kafafen sadarwa, sannan kuma a zo tare da wasu daga cikin jaruman film din. Ga mai neman Karin bayani kuma, zai iya ya nemar mu akan wadannan hashtags din a shafukan sada zumunta (social media):

#SadaukiTheEpicMovie
#SadaukiInCinemas
#Sadauki

Dangane da satar fasaha da gidan talabijin na Dadin Kowa StarTimes suka yi mana kuwa, kampanin shirya fina-finai na Giggs International na masu jan hankali na musamman akan su daina shelanta cewa zasu nuna film kaza a lokaci kaza matukar sun san basu da iko ko hakkin yin hakan. Ba daidai ba ne.

Shi kuma film din Sadauki har yanzu mallakin kampanin Giggs international ne shi kadai, kuma bai fita ba, balle a haska a Dadin KOWA StarTimes.

Har yanzu ana haskawa ne a iya sinima da wuraren da aka ware domin haskawa kamar dai yadda mu kayi bayani a sama.

Ma’assalam.

Las Danbuzu
FB/Twitter/IG/YouTube/SC – @danbouzu

Share with your friends
  •  
  •  
  •  
  •  
  •  
  •  
  •  
  •  
40 views

Leave a Reply

avatar