Budaddiyar Wasiqa zuwa ga Hassan Giggs: YAUSHE ZA’A HASKA SADAUKI A KANO?

#SadaukiTheEpicMovie #SadaukiInCinemas

A lokacin da na kalli film din #Hindu, wanda Darakta @HassanGiggs ya bada umarni, na fahimci cewa lallai masana’antar fina-finai ta @Kannywood ta fara shiga #NextLevel din da ake magana akan salon saddabaru wanda hatta Jakie Chan, na taba jinsa da kunne na yana cewa:

‘A lokacin da nake ganiyata a masana’antar shirya fina-fina ta Hong Kong, bamu iya yin saddabaru ba. Idan zamu yi wani abu na hatsari, sai dai ace mani ‘Rolling’, ‘Action’, sai inyi tsalle, daga nan kuma saidai na farka na ganni a asibiti.

Jakie Chan ya fadi wannan magana ne yayin bada amsa ga tambayar da wani babban mashiryin fina-finai na Hollywood yayi masa. Bayan shi baturen ya amsa wata tambayar da shi Chan din ya tambaya:

“Ya Luke kuna hada Kakannin kadangare (Dinosaurs) tare da mutane suke rayuwa a wuri guda?”

Sai baturen ya amsawa Jackie Chan da “ai ba wahala, saddabaru ne kawai, da an daddana computer shikenan an gama.”

Sannan sai shima ya tambayi Jakie Chan Lamar haka:

“Ta yaya take tsalle data wani gin zuwa wani ginin?”

Sai shima Jackie Chan yace

“Ai ba wahala, a zarar ance Rolling, Action, sai kawai nayi tsalle, daga nan sai asibiti.

Bayan wasu shekaru da kallon film din Hassan Giggs na Hindu, na je Film House Cinema a Kano na kalli #SARAUNIYA a cikin shekerar 2018, kuma na qara tsinkewa da al’amarin Babban Darakta Hassan Giggs.

A kwanan nan kuma shi dai Giggs din ya fara haska wani sabon shiri da ya sake bada umarni kuma ya shiryawa, wanda shima yake cike da saddabaru kamar sauran fina-finansa na baya. Amma sai dai a wannan karon yayi bala’in nuna qwarewa fiye da yadda ya nuna a baya. Wannan ya qara tabbatar mani da gaskiyar karin maganar nan na turawa wadda ake cewa ‘Practice make perfect’.

Wanna sabon shiri da nake baku labari sunansa #SADAUKI.

Saidai kash! Mashiryin wannan shirin wanda kuma shine babban mai bada umarni, wato Hassan Giggs yayi mani babban laifi. Wannan laifin kuwa yana da alaqa da karya al’adar #Kannywood da yayi ta fara hasko Sadauki a Maiduguri kafin Kano.

Bayan an kammala haska film din a Maiduguri, na gaggani a shafukan Social Media cewa za’a nuna film din ranar 25 ga wannan watan na Janairu a cinema. Da fari ina ta murna da doki akan zan dauki iyalina muje cinema din dake cikin Ado Bayero Mall a Kano mu wasa idanunmu, amma daga qarshe sai na lura ashe cinema din ba tamu ta Kano ba, ashe a cinema din #SilverBirdCinemas dake Birnin Tarayya Abuja.

Da muke tattaunawa da shi Giggs din da kansa akan ya zai yiwa Kano haka, sai yace mani ai ranar 25 ga watan Janairun ba a Abuja din kadai za’a nuna Sadauki din ba, har na fara murna, sai yace mani wai ai Kano sai nan gaba. Wai sai an fara da Zazzagawa kafin Kanawa. Wai za’a fara da Dove Event Center dake anguwar Kwangila a Birnin Zaria din, ranar 25, 26 da kuma 27 ga watan Janairu din. Kuma tabbabas hakan ya qular da in matuqa.

Kenan Hassan Giggs ya fifita Zazzagawa akan Kanawa?

To kenan mu ‘yan Katsina, a ina ya ajiye mu?

Tabbas mutanen Abuja da na Zaria sun rabauta, tunda aka zabe su da su fara kallon Sadauki kafin mutanen Kano, bare kuma mu jama’ar Katsina.

Kuma ina matuqar tayasu murna da zasu rigamu kallon wannan film wanda shine irinsa na farko ba wai a iya Kannywood ba, face a duka fadin Nijeriya. Domin shine shiri na farko a qasar nan da zaka ga namun daji tare da mutane suna rayuwa tamkar haka abin yake a zahiri.

Kuma shine irinsa na farko da akayi amfani da mutane marasa adadi, domin kuwa film ne dake nuna salon yaqe-yaqe irin na dauri, wanda zaka ga bangarorin mayaqa sun rugo aguje zasu yi ‘taho mu gama’ kai ka ce qudaje ne.

Daga qarshe dai ina tabbatarwa da Giggs yayi mana babban laifin da bazamu iya yafewa ba har sai ya cika mana wani sharadi guda daya..

YAUSHE ZA’A HASKA SADAUKI A KANO?

Las Danbuzu
FB/Twitter/IG/YouTube/SC – @danbouzu
20-01-2019

Share with your friends
  •  
  •  
  •  
  •  
  •  
  •  
  •  
  •  
44 views

Leave a Reply

avatar