MAULUDI: FAHIMTA FUSKA

By Faruk SarkinFada |

Hakika Manzo mai daukakar daraja, wanda ya kasance Rahama ga halitta, mai tausayi da jin ‘kai ga Muminai, ya zo mana. Duk da shudewar karni mai yawa bayan wafatin Manzon tsira, amincin Allah ya tabbata gareshi, yin bitar tasirin rayuwarsa da koyarwa tasa ta kasance abar fadakarwa da koyar da muhimman darussa ga duniya baki daya. Mafi darajar dukiyar da ya bari shi ne Alkur’ani da Sunna (hadisansa). Allah ya daukaka kiransa, ya kuma kiyaye koyarwarsa har izuwa karshen duniya.

Ga fahimtar wannan mai rubutu, mutane suna ganin Maulidin Annabi, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ta fuskoki daban daban gwargwadon fahimtarsu ga rayuwar wannan zinari a tsakanin duwarwatsu. A gurin mafi yawan mutane, Mauludi biki ne wanda ake yin sa duk shekara a watan Rabi’Awwal, amma tare da yawaitawa a ranar sha biyu ga watan. Wadannan mutane suna ganin Mauludi tamkar bikin tunawa da kewayowar ranar haihuwar Manzon tsira, ta hanyar yin bitar tasirin rayuwarsa da kuma yadda koyarwa tasa ta kasance abar fadakarwa da koyar da muhimman darussa ga duniya baki daya.

Wasu kuma sun fahimci Mauludi a matsayin ko wane irin aiki na nuna kauna ga Manzon Allah tsira da aminci su tabbata a gare shi, da kuma murnar bayyanarsa a cikinmu. Yin azumin ranakun Litinin yana daga cikin irin wadannan ibadu na nuna kauna da kuma ibada. An ruwaito cewar Manzon Allah tsira da aminci su tabbata a gare shi shima ya kasance yana azumtar ranakun Litinin domin tunawa da ranar haihuwarsa. A gurin wadanda suka dauki wannan fahimta, Mauludi abu ne wanda suke yinsa akai akai fiye da yadda masu yinsa sau daya a duk shekara. Sa’annan kuma wasu jama’a, suna yin murna ne da farin ciki bisa kasancewar Manzo a cikin mu kuma a tare da mu ta hanyar abubuwan da ya bar mana (Alkur’ani da Sunnarsa) ba kawai ranar haihuwarsa ba. Ubangiji Madaukakin Sarki ya ce:

“Ka ce dasu (Ya Muhammadu) da falalar Allah da Rahamarsa, domin wannan su yi farin ciki shi ne mafi Alheri daga abin da suke tarawa” (Kur’ani 10:58).

Alkurani mai girma shi ne Falalar Ubangiji da Rahama tasa. Amma kuma Manzon Allah tsira da aminci su tabbata a gare shi shi ne mafi zama Falala da Rahama ga Halittun Ubangiji.

“Kuma falalar Allah tã kasance mai girma a gare ka (Ya Muhammadu)” (Q4:113)

Bugu da kari:

“Kuma ba Mu aike ka ba (ya Muhammad) fãce dõmin wata rahama ga talikai” (Q21:107)

Masu wannan fahimta sun kasance tutur cikin farin ciki domin kasancewar Manzo, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi a matsayin Falala da Rahamar Ubangiji a cikin mu, ta hanyar Alkur’ani da Sunnar sa. Kamar yadda Manzon Allah, tsira da aminci su tabbata a gare shi ya kasance a dabi’unsa tamkar Alkur’ani ne shi mai kewayawa cikin mutane, haka a wannan zamani yake cikin mu a tare da mu matukar mun yi riko da Alkur’ani da Sunnarsa.

A wani bangaren kuma akwai daga cikin Musulmi ma su ganin Mauludi a matsayin wani abu ne fararre (watau Bidi’a) a cikin addini, wanda yake abin ki. Daga cikinsu akwai shahararren malami Sheikh Abdulaziz Bin Baz Ya fada cikin amsar wata Fatawa kan Mauludi cewar:

“… abin da muka sani daga Shari’a mai tsarki kuma masu Hakikancewa daga cikin ma’abota sani suka tabbatar dashi shi ne yin Mauludi Bidi’a ne, babu kokwanto. Domin Manzo tsira da aminci su tabbata a gare shi wanda ya fi kowa nasiha da sanin Shari’ar Ubangiji da kuma kaiwa matuka wajen Ubangiji, bai yi Mauludinsa ba. Kuma sahabbansa da Kahlifofinsa shiryayyu (ko wa]ansun su), ba su yi Mauludi ba. Yau da Mauludi ya kasance gaskiyane, ko alkhairi ne, ko sunna ne, da sun zabura izuwa aikatashi. Amma tun da Annabi tsira da aminci su tabbata a gare shi ya bar shi, bai yi shi da kansa, kuma bai koyar da Sahabbai da Khalifofi da sauran Al’umar sa kan yin sa ba, to mun sani babu shakka ba shi daga cikin Shari’a. Kuma Hakika Manzo tsira da aminci su tabbata a gare shi ya ce: “Wanda ya farar da wani abu a cikin wannan al’amari namu, wanda bai zamo daga cikinsa ba, to shi (aikin) abin juyarwa ne.” Ya kuma ce a cikin wani Hadisin: Duk wanda ya yi wani aikin wanda ba mu muka yi umarni ba, to shi abin juyarwa ne.”

Masu ganin kyautuwar yin Mauludi suna dangana kasancewarsa bidi’a ce mai kyau daga cikin bidi’o’i, kamar yadda Sheikh Usman Bin Fodiyo ya bayyana rabe-raben bidi’a a cikin littafinsa ‘Ihyau’s-sunnah Wa Ikhmadul Bid’ah’ (Dubi shafi 11-15). Cikin wannan littafi ya yi bayanin ma’anar bidi’a da rabewarta izuwa kashi biyar, watau Wajiba, Muharrama, Mandubiya, Makruhiya da kuma Mubaha: Ya ce:

“Ahmaduz-zaruki ya fada a cikin littafinsa Umdatul Muridis-sadik. Hakikanin bidi’a a Sharia shine farar da wani abu a cikin addini wanda ya yi kama da addini amma ba ya daga cikinsa”

A cikin wannan bayanai, ya kawo misalai da dama a kowace nau’in bidi’a. Domin takaitawa, na kawo misali daya tak na kowace nau’in bidi’a. Bidi’a Wajiba itace abinda ya dace da ka’idojin wajabci a bisa dalilan Sharia. Misali, tattare Alkur’ani mai tsarki da Shari’o’i, yayin da aka ji tsoron tozartarsa. Bidi’a Muharrama ita ce abinda ya dace da ka’idojin haramci bisa dalilai na Sharia. Misali, gabatar da Jahilai bisa masu Ilmi. Bidi’a Mandubiya ita ce abin da ya dace da ka’idojin mandubanci bisa dalilai na Sharia. Misali sallar Tarawi. Bidi’a Makruhiya itace abin ya dace da ka’idojin Karhanci bisa dalilan Sharia. Misali yin kari a bisa adadin ibadah mandubiya kamar zarcewa bisa karanta tasbihi talatin da uku bayan sallar farilla. Bidi’a Mubahiya itace abin da ya dace da ka’idojin halarci bisa dalilan Shari’a. Misali yin musafaha bayan sallar Asubahi da La’asar.

Sheikh Al-Isbali, cikin sharhin Arba’una Hadith ya ce: Ayyuka muhaddasai (fararru) sun kasu kashi biyu,: Marasa kyau, wa]anda ba su gini a kan dalilai na Shari’a ba da kuma masu kyau, wa]anda suka ginu a kan dalilai na shari’a. Misali, a yayin da Sayyadina Umar (RA) ya ga ana yin Sallar Tarawih cikin Jama’a sai ya ce: “Madalla da wannan Bidi’a”.

Bugu da kari Sheikh Ibrahim Lakkani ya ce a cikin littafinsa Kitabul manarul fatawa cewar yana daga girman jahilci mutum ya dauka cewa duk irin aiyukan da ba a aikata su zamanin Sahabbai ba bid’a ce abar ki. Misali neman Ilimin Fiqhu da Usulud-dini bid’o’i ne wajibai. Hakanan Manzon Allah tsira da aminci su tabbata a gare shi ya ce: “Wanda duk ya sunnanta wata sunnah mai kyau, to yana da ladanta da kuma ladan wanda ya yi riko da ita har izuwa ranar Alkiyama. Haka nan wanda duk ya sunnanta wata sunnah mummuna to yana da zunubinta da zunubin wanda ya yi riko da ita har izuwa ranar tashin kiyama”

Don haka muna iya duban Mauludin Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ta fuska biyu. Zai iya kasancewa bidi’a kyakykyawa matukar duk abin da aka gudanar a cikinsa ya dace da abin da Shari’a ta yarda da shi. Amma kuma zai iya kasancewa abin ki idan aka gudanar da abin da ya sabawa Shari’a yayin aikata shi. Allah shi ne mafi sani.

Hakika Manzo mai daukakar daraja, wanda ya kasance Rahama ga halitta, mai tausayi da jin kai ga Muminai, ya zo mana. Muna Marhaban da Manzon da ya zo mana cikin wa]annan baitoci:

Ka yi min izini da na dan matso
A cikin tafkinka na sha na tso-
tsi diyan bishiyarka, a ce na tso-
ma kafa haskenka a ce matso
Huta inuwar ba shan wuya.

Domin rai na zai tsarkaka
Ruhi ya zamo mai daukaka
Na sami abokin nanaka
Cikin tsara na ba shaka
Na zamo tauraro kwal daya.

Kiranka kadai naka bibiya
Bani juyayi ko waiwaya
Na baro aikina na tsaya
Na nufo ka kadai ba waiwaya
Kai kadai naka so ba kishiya.

Ban jin sanyi, zafi, bare
Iska da ruwa ko ko dare
Tunda ga doki na zan dare
So nake ka zamo tamkar zare
Kullalle tare da zuciya.
Alhamdulillahi

(c) Faruk Sarkinfada
12/12/2017

Share with your friends
  •  
  •  
  •  
  •  
  •  
  •  
  •  
  •  
76 views

Leave a Reply

avatar