ZUWAN SANATA KWANKWASO KANO

Maganar gaskiya ko kadan ban yi niyyar cewa komai game da zuwan tsohon Gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso Kano da kuma fasa zuwan da yayi daga baya ba, hasalima duk da ni dan jihar Kano ne, amma a baya – bayan nan ban fiye shiga harkokin siyasar Kanon ba, ba wai don bana so ba, a’a sai don aiki na, da kuma yadda na lura da wanda nake yi wa aikin, Shugaba Muhammadu Buhari bai dauki bangare ba, ya dauki kowa a matsayin na sa.

Sai dai a dan baya-bayan nan, na ga akwai kwararen dalilin da ya kamata nayi magana, tun bayan da Sanata Kwankwaso ya sanar da fasa zuwan sa Kano kamar aka tsara a baya, sai wasu mutane musamman daga cikin magoya bayansa suke alakanta ko daura laifin rashin zuwan na sa akan Shugaba Muhammadu Buhari, wanda ko kadan hakan ba gaskiya ba ne.

Shugaba Buhari bai hana Sanata Kwankwaso zuwa Kano ba, jami’an tsaro suka ba shi shawara, saboda dalilai na tsaro.

Shin menene zai sa Shugaba Buhari ya hana Kwankwaso zuwa Kano?

Ga duk mai tunani ya san ba dalilin da Shugaba Buhari zai hana Kwankwaso ko wani zuwa ko’ina a fadin kasar nan. Shin idan gaskiya ne ya hana shi zuwa Kanon, me yasa bai hana shi zuwa sauran jihohin da yake ta zuwa ba, a kwanan nan Kwankwaso ya ziyarci jihohi da dama ciki har da jihar Katsina, mahaifar Shugaba Buhari, idan har bai hana shi zuwa Katsina ba, me zai sa ya hana shi zuwa Kano.

Idan kuma suna tunanin saboda zaben 2019 ne, mai ya sa Shugaba Buharin bai hana tsohon mataimakin Shugaban Kasa, Alhaji Atiku Abubakar zuwa jihar Adamawa da sauran jihohin da yake ziyarta ba, ko kuma Sule Lamido da Mallam Ibrahim Shekarau wadanda a koda yaushe suke ziyarce – ziyarcen su duk inda suke so.

Daga bangaren mu har gobe muna ganin girman Sanata Kwankwaso a matsayin sa na daya daga cikin manya a jam’iyyar mu ta APC.

Ina fata a koda yaushe zamu ke yin maganganu masu hujja, kar soyayyar siyasa take rufe mana ido, muna sa son zuciyar mu, domin kuwa hakan ba zai haifar mana da mai ido ba.

Na gode!

Bashir Ahmad
Maitaimakawa Shugaba Buhari
Kan Sababbin Kafafen Yada Labari

Share with your friends
  •  
  •  
  •  
  •  
  •  
  •  
  •  
  •  
250 views

Leave a Reply

avatar