Ba na Tausayin Mutanen Kauye

Daga Auwal DanBorno

Ranar Lahadin da ta gabata, mun je Katsina domin halarta taron Shirye shiryen Ranar Marubuta. Tun wajen kamar Sha daya na rana mu ka fara taro, ba mu kammala sai wajen karfe shidan Yamma. Taron bayan taro gaishe gaishe da Salloli ya sa mu ka shafe wajen Rabin awa. Bakwai saura dai mu ka dauki hanya. Na so na kwana saboda barci da na ke ji,amma da yake na dauko Jamilu Haruna Jibeka tun safe a gidansa na hakura da kwanan. Na San Matar sa da wuya ta amince saboda tun farko ba su yi da ita zai kwana ba.Izinin da ya tambaya na wuni guda ne.
Ga dai barci ina ji,amma kasancewar tare na ke da Jamilu Jibeka sai ya zama hirar da mu ke ta kori barcin.

Muna tafe muna ta wuce Kauyuka manya da kanana, mu ka zo wani gari mai duhun gaske. Babu hasken wuta ko na acibalbal sai tocila tsalli tsalli da wasu ke haskawa daga gefe. Ban iya gane Kauyen yana karkashin karamar hukumar Kankia ko kusada na jihar katsina, ko kuma Karamar hukumar Tsanwaya ta kano da ke iyaka da Katsina. Ban kawo komai a raina ba,amma dai na ji hirar da Jamilu ke yi min ta tsaya. Dama hira ce ya ke min ta rasuwar Yayansa Muktar Wanda abokina ne, tare mu ka yi Firamaren Gobirawa da ke kano da Karamar Sakandiren Kofar ruwa. Mun rabu a Babbar Sakandire. Na tafi SAS kano shi kuma ya gama a Gwammaja 2 ko 1.

” Gaskiya Danborno duhun garinnan ya yi yawa.”

” Hmmn Ashe ka lura.!”

” Kwarai ma kuwa , ni fa ina mugun tausayawa Mutanen Kauye”

” Ikon Allah me ya sa kake tausaya ma su?”

” Ai dole a tausaya ma su saboda rashin kayan more rayuwa da wahala da su ke ciki”

” Gaskiya kam,amma ni raayina da banbanci da na ka”

” Menene banbancin?”

” Ina jajanta ma su rashin kayan more rayuwa daga gwamnati,amma ni ba na tausayin su.”

” Ba ka tausaya ma su?”

” Menene abin tausayin?”

” Kai ba ka ganin dawainiya da bakar wahala da su ke sha. Sai sun duka sun noma sannan su sami Dan abinda za su ci su ciyar da yaran su haba.”

” Jamilu mutanen kauye da kake gani kaso saba’in a cikin Dari su na Jima’i da haihuwa,amma ba su ke daukar dawainiyar Yayan ba. Babu Wanda ya fi mutanen kauye auri saki da yawan haihuwar yaran da ba su iya kula da su. Duk wadannan yaran da kake gani wai ana kawo su da sunan karatun Allo da yawan su karyar banza ce karyar wofi. Wallahi da dama kawai su na turo su ne domin saukakawa kawunan su dawainiyar ciyarwa da kuma yau da gobe.
Wannan ta Sanya za ka ga ba su damu da Tara matan ba,abinci ga shi nan a rumbu,dakuna kuma ga su nan da kasa ake yi, kasar kuma hakota ake yi a Mahakar kasa. Tumba da Azara duk ga su nan a daji. Amfanin Yaran da su ke haihuwa shine duk shekara su taya su noma abinda za su ci da Wanda za su sayar su yi cefanen shekara, idan rani ya yi su turo mana yaran mu ciyar da su daga cikin abinda mu ka saya da albashin mu a wajen Iyayen su.

Ba ka lura ba ne wai, yaro daga an yage shi daga nono sai nan da nan a yi masa kaciya, tun kafin ya gama warkewa an hada kayan sa na tafiya almajirci. Kai ba ka ganin yara yan guyan Guyan a danjoji cikin Birane . Idan da gaske karatu ake kawo su saboda Allah, mai zai hana a hado su da suturar sanyawa ,abinci,omo na wanki da sabulun wanka da man shafawa. Me zai sa duk sai sun zo sun yi barar duk wadannan kaya. Idan da gaske karatu ne dalilin zuwan su, mai zai hana su bar su a garuruwan su ko gari mafi kusa da su. Wanne gari ne yanzu babu Mahaddacin kur’ani ko mai kyakkyawar tilawar da zai iya karantarwa. Me zai su dinga zama a kauyuka idan da gaske karatu su ke zuwa ba kwadayi a cikin birane ba. Ta yaya zan ji tausayin azzaluman mutanen da ke iya tura yaro Dan shekaru bakwai garin da ba su San yadda yake ba. Ya zan tausayawa azzalumin da zai iya kwana yayi barci gami da jima’i cikin jin dadi ba tare da ya San yadda Dan sa ya ci ya sha ko bai San ya makwancinsa ya ke ba. Ba na tunanin akwai rashin inamin da ya kai na mutum ya fincike Dan da ya Haifa daga cikin sa ba tare da yasan . Bari na ba ka wani labari da Hamza Dawaki ya ba ni kamar shekaru biyar da su ka wuce na wani yaro Almajiri

2
Hamza ya ce, an taba kawo ma sa wani almajiri bai da lafiya magashiyyan. Zazzabi ne na typhoid mai tsananin zafi da yake bukatar kulawa ta musamman. Ga shi kuma Malaman sun ki bayar da kudade domin a duba lafiyar yaron sosai, sai kame kame su ke yi. Da ya tambayi ko ina iyayen yaron sai Malamin ya ce an kira shi ya ki zuwa. Wai in ji Malamin yaron ya takurawa Amaryar da babansa ya auro bayan ya rabu da Uwar yaron, shi ya sa ya kawo shi makarantar Allo kenan saboda ya yi Jima’in sa yadda yake so.
Ga duk Wanda ke da alaka da mutanen Karkara, ya San daga Kaka ta yi amfanin gona ya samu, ba su da wani Abu da ya wuce aure aure. Bazawara daya ko Budurwa, sai ka same ta da manema sama da biyar, kuma wani rashin mutunci babu Wanda ya San wanda za ta aura sai ranar auren. Higher Bidder su ke dubawa ba wai mai mutunci ko kyakkyawan asali ba. Bisa wannan dalilin ya sanya za ka ga yawan auri saki da rashin mutunci da wulakanta kima da darajar mace ya fi ga mutanen kauye.Abinda da damar mutanen kauye ke daukar Matayen su shine injin Sauke shaawa da bugo ma su yaran da za su turo Birane Bara . Na taba samun wani labarin wani mutumin kauye. Matar sa za ta haihu Dan ya fara fitowa sai ya makale. Aka yi ta jike jike Matar ba ta sami sauki ba yaron kuma bai fito ba. Da kyar aka shawo kansa ya kai ta asibiti wai bai da kudi. Malaman Asibiti su ka rubuta ma sa abubuwan da zai saya wallahi da ya karbi takardar sai ya gudu.

Allah ya sa maaikatan asibiti sun cigaba da aikin ba tare da sauraren zuwan sa ba. Cikin taimakon Allah matar ta haihu. Malamar Asibitin ta ce abin haushi, wai sai ga mijin da yamma likis da Makara da wa su tsofi wai a ba shi Gawar Matar sa. Mamakin da Malaman asibiti su ka yi ya wuce misali. Wa fada ma sa matar ta mutu, shin ya gudu ya bar ta ne domin ta mutu ko kuma dama ba ya kaunar ta. Irin wannan halin dabbancin sai ka rasa ta ya mutum mai hankali zai yi irin wannan.”

” Wai Ag ba wata hanya da kake ganin zaa hana irin wannan turo Almajirai Birane.?”

3
Nasir Sulaman yace A shekarar 2009 na duba research na Msc project da wani malami na yayi a wannan mas’ala, conclusion ya nuna cewar kaso 80 daga cikin 100 na miyagun mutane masu munanan d’abi’un da suka had’a da fashi da makami, fyad’e shaye-shaye duk irin wad’annan yara ne da ake kawowa daga karkara zuwa birane da sunan neman ilimin al’qur’ani amma a xahiri ba manufar kenan ba.

Last week naji hira da wani professor yana magana koda wad’anda aka yi sa’a k’addara ta rubuta cewar zasu girma su zama mutane masu wata baiwa ko ta kud’i ko ilmi ko d’aukaka to dayawa daga cikinsu zakayi tsinkaye basu tausayin al’umma saboda suna tuna yanda iyayen su suka haife su sukayi watsi da su kuma duniya da al’umma suka wofantar dasu a lokacin da suke bukatar tallafin su.

Malamai masana a fannin social psychology/ ilmunnafs sun tabbatar da cewa ba yin jima’i da haifar jariri ne yake samar da shaquwa da jin k’ai daga ‘ya’ya zuwa iyaye ba, kulawa da tarbiyantarwa da ilmantarwa shine yake haddasa feelings na jin k’ai da tausayi gami da kyautatawa daga ‘ya’ya zuwa iyaye.

Idan kuwa haka ne taya iyayen da suka haifi yara suka watsowa duniya da zummar ta cigar dasu ta tarbiyantar dasu zasu tsammaci jin k’ai daga wajen su?

“Hana wanna tsari dole sai Gwamnati ta sanya hannu. A kwai wani tsari na tsangaya da Malam Shekarau ya dauko a shekarun baya, na sanya hannun gwamnati wajen gudanar da Makarantun Allo. Da a ce wannan tsari ya dore ta zaa yi amfani da shi wajen sa wa Malaman dokoki da tsari. Amma duk wannan surutun da mu ke yi ba za su sauya ba.

Ana samun da yawa su su na fandarewa su bi mummunar hanya ,ko Shiga cikin ma su aikata manyan laifuka. Dalilin bai wuce tashi da su ka yi ba kulawa ko kwaba idan sun aikata wani Abu da ba daidai ba babu Wanda zai tsawatar nasiha ko nusarwa. Da yawan su ko sun girma za ka same su da zuciya a kekashe, saboda wuyar rayuwar da su ka sha a lokacin da su na yara.

Abin haushi har yanzu ana danganta wannnan dabia ta wulakantar da Yara da sunan addini. An kasa haduwa a gyara lamarin,kowa tsoro ya ke ji kar a ce ya taba Malaman addini. A bangaren Malam kuma, za ka samu da yawan su ba sa Dora yaran bisa turba ta shariar addinin musulunci, ba sa koyar da su ilmin addini sai dai kawai kurman karatun kur’anin da ba bisa Ka’ida ba.

Yadda su ke duka da tsangwamar yaran yana daya daga cikin hanyoyin da ke sanya zuciyar Yaran ta kekashe.

Wani abin lura da ya sa mutanen kauye ba za su daina bin wannan hanya ba shine; bayan samun saukin rayuwa, sun fahimci cewa yaran nan fa idan Allah ya sa su ka tsallake wannan kunci da wahalar rayuwa , su ke zama manya manyan yan kasuwa. Kuma haka ne. Duk kasuwannin mu idan ka duba Irin wadannan Almajirai su ne manyan Yan kasuwa. Da wuya ka ga wani shahararren Dan boko ya shahara wajen gudanar da kasuwanci sai guda guda. Da yawan manyan yan kasuwa za ka ji su na fadin sun fara da daukar dako ko makamancin sa.

Wajen da za ka sha Mamaki, da yawan Iyayen nan da ke turo su Almajirci ba su cika amfana da dukiyoyin na su ba. Shi ya sa da yawa za ka ga yaron mutum ya zama babban Dan kasuwa,amma uban na kauye na ta wahala irin wadda ya saba a baya. Wannan ya samo asali ne daga rashin shakuwa da kuma rashin daukar dawainiya da kuma nesanta da su ka yi da juna.

Da yawa ba su cika tashi da tausayi ba, sai Wanda Allah ya tsare. Su na kasancewa kamar su na fushi da alummah ne saboda yadda su ka shiga kuncin rayuwa a baya. Wani abin takaici da haushi , duk lokacin da aka fara maganar kawo gyara a harkar Almajirci sai ka ji wasu da ba su tura yayan su ba sun fito su na kare abin da sunan Addini. Shekarun baya Malam Adamu Aliyu Kiyawa a shirin sa na Birgimar Hankaka ya dauko maudu’i kan Almajirai da yadda zaa gyara harkar. Abin Mamaki sai ga shi wasu sun fito da Makara ta daukar Gawa wai za su yi ma sa Alqunut, wai ya na taba Addinin Allah.

Idan ka dubi wannan harka ta turo yaran da ko tsarki ba su iya ba, sai abin ya sa ka zubar da wahaye. Wa ke ma su wanka ,a ina su ke kwana musamman yanzu a lokacin sanyi. Manshafawa sabulun wanka ,omo na wanki da Man goge baki baa maganar su.

Abinda zai ba ka mamaki ka San ba wai karatu ke kawo su Birane ba shine; Su ma fa Malaman da ke yawo da su mutanen Kauyen ne. Idan haka ne mai zai hana su bude makarantun a garuruwan da su ke su dinga koyarwar. Mai zai sa su zo wajen da ba su da gidaje sai dai shagunan mutanen unguwa da soraye. Babu bandakuna sai dai su dinga kashi da wanka a kangwayen mutane. Wannan muzanta sunan addini da ake yi ya yi yawa .

Ta ya Malamin da ke kula da Almajirai sama da Dari biyu zai iya kula da lura da tarbiyyar su. Idan dayan su bai kwana a makaranta ba ta ya zai gane. Wannan Malamin ta ya zai San wajen da Almajirai ke zuwa Neman abinci ko waje ne da idan su na zuwa tarbiyyar su za ta gurbata. Wai ina Hankalin mu ya ke, ina marubuta Manazartan mu su ke. Shin da Gaske ne alkami ya fi takobi . Ya zamu mayar da hankali wajen rubuta soyayyar banza da zuga yaran mutane su na fadawa Rijiya. Ga dai abu cikin alummar mu Wanda ya ke kawo rashin cigaba ,amma mun yi shiru kawai mun zuba ido. Kullum idan aka tashi lissafin koma baya sunan alummar mu ne a gaba,sunan yankin mu ne kan gaba.
Ga dai kasar Noma Allah ya hore, amma Dan iskanci duk sun turo yaran Almajirci,yankan Farce ,wankin Takalmi dss. Duk kauyukan da ka je sai ka tarar da kaso shida cikin goma, na gonakin su ba sa noma su, saboda lalaci da kwadayi da son yawo ko zama cikin birane. Idan an yi magana sai su ce Gwamnati ba ta bayar da tallafi ba. Na sha tambayar mutanen kauye cewa , lokacin da kakannin mu su ka yi Noman da aka yi amfani da shi wajen Gina Najeriya wa ya tallafa ma su da Takin zamani. Shekarar da ta wuce an ba da rance ga manoma, ina jin lokacin biya ya yi amma har yanzu da yawa ba na tunanin sun biya. Wa su ma ba noman su ka yi ba.
Dole ne a dage da rubuce rubuce da waazi daga Malaman kan wannan mummunar Akida idan har ana so a yi gyara a daina lissafa mu a cikin koma baya.

Tammat.

Share with your friends
  •  
  •  
  •  
  •  
  •  
  •  
  •  
  •  
871 views

Leave a Reply

avatar