Kisan Bilyaminu: Wataqila a saki Maryam Kwanan nan

By Gimbiya Nana Nuratu:

Wannan hotuna da kuke gani, shine gidan marigayi Bilyaminu wanda ya rasa ransa sakamakon tashin hankalin da ya barke tsakanin shi da mai dakin shi wato Maryam, wata majiya mai tushe ta baiyana cewa tabbas ita Maryam batayi anfani da wuka kamar yanda ake ta yadawa ba wajen kashe mijin nata ba.

Mai maganar yace fada ne ya barke tsakanin su bayan shi abokin Bilyaminu ya fita waje don yayi waya inda yajiyo ihu a cikin gidan, koda ya koma sai ya iske Bilyaminu a kan maryam, kuma wai dalilin mutuwar shi Bilyaminun, zamewa yayi ya fadi a kan kwalban Shisha da ya fashe wanda shine yayi sanadiyar ajalinsa, bincike ya nuna ko kafin su isa asibiti tuni Bilyaminu ya rasu, yanzu haka dai maryam na tsare, mahaifin marigayin wai yace a sake ta amma mahaifin ta yace a’a, aci gaba da tsareta har sai an kammala bincike.

Sanadiyar wannan al’amari dai shine wane ‘text message’ ne da ita maryam d’in ta gani a cikin wayar mijin nata daga wata budurwa.

Allah ya kyauta.

Share with your friends
  •  
  •  
  •  
  •  
  •  
  •  
  •  
  •  
425 views

Leave a Reply

avatar