MATAR BILYAMINU: KISHIN MATA ‘YAN BOKO A AREWACIN NIJERIYA


By Muhammed Ibrahim.

Lamarin nan bai fara da matar nan da ake zargin ta kashe Bilyaminu ba, ke nan ba zai qare da ita ba. Lamari ne da yake neman zama ado ga mata ‘yan boko a arewacin Nijeriya, cewa dole wai su ne masu sa ido a kan mazajensu, ba mazajen ne masu sa ido a kansu ba. Abin baqin cikin kuma, wasu talasuran mazaje da sunan “wayewa” suna barin matan na yin yadda suka so.

Kafin shekarun saba’inoni, kai har ma zuwa tamaninoni, mata a qasar Hausa, sun yarda kuma sun aminta da cewa su d’in nan, biyu-biyunsu, ko uku-ukunsu, ko hud’u-hud’unsu, ababen aure ne a jumlace ga mutum guda. Hakan ya sa akwai qarancin matsalolin kishi makamancin wannan da ke sa kisa a wancan lokaci. Saboda a cikin qwaqwalwa da zuciyar mace, ta san ko da ita ce ta fara shiga gidan mijinta, to fa qofar shigowar wata ko wasu ba za ta garqamu ba.

Amma a yau, aqidar boko da d’abi’un ‘yan Kudu sun sa za ka ga lafiyayyen mawadacin namiji, yana ganin wayewa a cikin zama da mata guda, rashin wayewa kuma a tara mata, duk kuwa da cewa yana da tulin ‘yan mata a waje. Hakan na daga cikin sabubban da ke sa matan na ganin ai ma haqqinsu ne su zauna da mazajensu su kad’ai. Kuma duk namijin da ya nemi sa’ba wa hakan, sunansa maqiyi. Maqiyi kuma maganinsa kashewa. Don haka ma sai aka wayi gari ana kallon, son da namiji mai mace guda zai yi wa wata macen daban, cin amana ne.

Yadda a zahiri halittar namiji ta sha bamban da ta mace, haka hatta a qwaqwalwa da zuciya, lissafin namiji ya sha bamban da na mace. A tsarin halittar mace, in ji masana, ba ta iya so ko buqatar fiye da namiji guda a zamani guda. Amma a tsarin halittar namiji, yana iyawa. Wasu masanan ma sun ce namiji ya fi samun daidaito (balance) idan yana da fiye da mace guda.

A shafi na 80 na littafinsa The Pleasures of Philosophy, Will Durant ya ce: “Ko shakka babu yana daga cikin d’abi’unmu da ba sa canzawa, son mata daban-daban, tsarin halitta bai gina mu don zama da mace guda ba.”

Share with your friends
  •  
  •  
  •  
  •  
  •  
  •  
  •  
  •  
210 views

Leave a Reply

Be the First to Comment!

avatar