GAME DA DUBA WAYAR MIJI

By Auwal DanBarno.

Na taba fadawa Matata cewa; Bai halatta ba ki duba wayoyina, domin akwai sirri tsakanina da wasu. Kuma ba ni a karkashin kulawar ki. Amma ke ya halatta na duba wayoyin ki, domin kina karkashin kulawata kuma ni kadai ne mijin ki.

Sai ta tambaye ni cewa; idan aka tambaye ta wannan fatawar wanne Malami ce ya za ta CE. Ban amsa wannan tambaya ba har yau.

Na sha fadawa Mata cewa Namiji na da wasu damarmaki fiye da su. Akwai abinda Namiji zai tattauna da wata, idan matar ta gani ba za ta ji dadi ba.

Ba Ina nufin wai tattaunawa ta iskanci ko batsa ba. Tattaunawar da ta halatta, misali. Ina Neman aure zan Kara ,Yarinyar kullum na je zance da Hijabi burmeme ta ke fitowa. Malamai kuma sun sha yin Bayanin halaccin ganin wani bangare na jikin Matar da mutum ke son aure. Sai wataran da na je zance da sa ta cire Hijabin domin na Dan dudduba abinda ya yi min. Ta bude na duba,amma ba ta iya jin raayina ba a lokacin ido da ido saboda kunya. Sai da na je gida sai ta turo sako misali ta WhatsApp.

” Honey ka sa na tube Hijabi ba ka ce komai ba,bayan ka dudduba”

” Ayyah Baby ai ba magana. Komai ya ji,babu wani Abu na jikin ki da bai burgeni ba, musamman kaufrinki da na ga babu tabo ko daya.”

” Kai amma na ji dadi da ka yaba Sha Allah za ka same ni cikakkiyar mace ”

” Haha Dear kenan ai ko yanzu ga dukkan alamu samun Mace kamar ki abu ne mai wahalar gaske.”

Wannan hirar da dubawar duk ba Wanda ya sabawa Sharia a fadin Malamai. Amma idan da a ce matar mutum za ta bincika ta gani,sai wannan zancen ya zama kamar Ma fi girman zunubi da baa taba aikata kamar sa ba. Abinda kuma ba ta sani ba shine; Wannan duba waya da ta yi ba karamin alhaki ta dauka ba.

Ya kamata Mata su dinga hakuri da bin diddigi da leken asiri. Namiji in ji Hausawa mijin Mace hudu ne.

Share with your friends
  •  
  •  
  •  
  •  
  •  
  •  
  •  
  •  
198 views

Leave a Reply

Be the First to Comment!

avatar