Qur’anin ‘Yan Shia

By Abdulrahman Murtala.

Qur’anin ‘yan Shia; yana da surori 114. Ayoyi 6236. Kalmomi; 77,439. Harrufa; 323,015. Juzi’i; 30. Hizfi 60. Rubu’i 240. Ushuri 480.

Surorin da aka saukar a Makkah a Qur’anin ‘yan Shia; 85 ne. Surorin Madinah; 29 ne. Surarin da suka fara da ‘Alhamdu’; 5 ne. Surorin da suka fara da Tasbihi; 6 ne. Surorin da suka fara da harrufa; 19 ne.

Surah da ta fi tsawo a Qur’anin ‘yan Shia ita ce; Suratul-Baqara, ayoyin ta 286.

Aya mafi tsawo a Qur’anin ‘yan Shia ita ce aya da tayi magana akan bashi, aya ta 282 a Baqara, kalmomin ta 128.

Kalma mafi tsayi a Qur’anin ‘yan Shia ita ce; ﻓَﺄَﺳْﻘَﻴْﻨَﺎﻛُﻤُﻮﻩُ (Fa’asqainaakumuhu), (Hijir : 22), tana da harrufa 11 a rubutun ta na larabci.

Qur’anin ‘yan Shia; an saukar da shi cikin shekaru 23.

Qur’anin ‘yan Shia yana da sunaye kamar haka: Al-furqan, At-tanzeel, Az-zikir, Al-kitab, Al-wahayi, Ahsanul Hadith, As-siradul Mustaqim, Al-urwatul Wuthqa, Ar-ruhu…

Qira’ar da tafi shahara wajen karata Qur’anin ‘yan Shia ita ce ruwayar Hafs daga Asim…, (Qira’ar da isnadita yake tukewa zuwaga Imam Ali(as). Hafs ya bar duniya a shekara ta 180 H, Asim kuma 127H.

Annabin da aka fi ambaton sunan sa a Qur’anin ‘yan Shia shine; Annabi Musa(as); a ambace shi sau 136.

Surorin da aka ambace su da sunan dabbobi a Qur’anin ‘yan Shia; Baqara (Saniya), Namli (Tururuwa), Ankabut (Gizo-Gizo, Nahli (Zuma), Fiyl (Giwa)…

Surorin da aka ambace su da sunayen Annabawa a Qur’anin ‘yan Shia; Suratu Yusuf(as), Suratu Hud(as), Suratu Ibrahim(as), Suratu Muhammad(saw), Suratu Nuh(as), Suratu Yunus(as)…

Surorin da aka ambace su da sunayen taurari a Qur’anin ‘yan Shia; Suratut Najm, Suratul Qamar, Suratud Dariq, Suratush Shams, Suratul Buruj…

Surorin da aka ambace su da sunayen lokuta a Qur’anin ‘yan Shia; Suratul Fajr, Suratul Laili, Suratud Dhuha, Suratul Asr…

Tsuntsaye da Dabbobin da aka ambace su cikin Qur’anin ‘yan Shia; Al-ba’ula (Sauro), As-Salwa, Al-Guraab (Hankaka), Al-Jarad (Fara), An-Nahl (Zuma), Az-Zubab (Kuda), Al-Baqara (Saniya), Zubaab (Kuda), Namli (Tururuwa), Al-Hudahuda, Naaqah (Raquma), Khail (Doki), Al-Bighaal (Alfadari), Al-Himar (Jaki), Az-Zi’b (Kyarkeci), Al-Kalb (Kare), Al-Fil (Giwa), Ankabuut (Gizo-Gizo, Al-Ibil (Rakumi)…

Sunayen Mala’ikun da suka zo cikin Qur’anin ‘yan Shia; Jibril(as), Mi’ika’il(as)…

Daular da aka ambata a Qur’anin ‘yan Shia ita ce; daular Rumawa – Rom,

Qabilar da aka ambata a Qur’anin ‘yan Shia ita ce; Quraishawa – (Quraish).

Littattafan Tafsiri da suka fi shahara a wajen ‘yan Shia; Al-mizan – Tabtaba’i, Tafsirut Tabari, Tafsiru Ibn Kasir, Tafsiru Ruhul Ma’ani – Aluusi, Tafsirul Qurdabi, Tafsiru Mafaatihul-Gaib…

Gurare 4 sunan Annabi Muhammad(saw) ya zo kakara a Qur’anin ‘yan Shia: Aali Imran aya ta 144, Ahzab aya ta 40, Muhammad aya ta 2, Fathi aya ta 29.

Qur’anin ‘yan Shia: littafi ne da Allah(swt) ya saukar wa Annabi Muhammad(saw), wanda Allah(swt) yayi alkawalin karewa daga canzawa ko jirkitawa.

Yarda da cewa akwai wani Qur’ani daban da Qur’anin da Allah(swt) ya saukarwa Annabi Muhammad(saw); tamkar karyata ayoyin da suka tabbatar da cewa ba wanda ya isa ya iya kirkirar wani littafi irin Qur’ani:

Tabbas ayoyin Qur’ani sun tabbatar mana da cewa ba zai yiwu a canza Qur’ani ko a kirkiri wani irinsa ba:

Allah(swt) a Suratul-Hijr Aya ta 9, yana cewa:

ﺇِﻧَّﺎ ﻧَﺤْﻦُ ﻧَﺰَّﻟْﻨَﺎ ﺍﻟﺬِّﻛْﺮ ﻭَﺇِﻧَّﺎ ﻟَﻪُ ﻟَﺤَﺎﻓِﻈُﻮﻥَ

“Tabbas mu muka saukar da Qur’ani sannan tabbas mu ne zamu kareshi..”

A wannan ayar Allah(swt) yana tabbatar mana da cewa ba wani dan Adam da zai iya kara wani abu a cikin Qur’ani, saboda Allah yayi alkawalin kare Qur’ani.

A wata ayar Allah(t) yana cewa:

ﻟَّﺎ ﻳَﺄْﺗِﻴﻪِ ﺍﻟْﺒَﺎﻃِﻞُ ﻣِﻦ ﺑَﻴْﻦِ ﻳَﺪَﻳْﻪِ ﻭَﻟَﺎ ﻣِﻦْ ﺧَﻠْﻔِﻪِ ۖ ﺗَﻨﺰِﻳﻞٌ ﻣِّﻦْ ﺣَﻜِﻴﻢٍ ﺣَﻤِﻴﺪٍ .

“Barna (canji) ba ya zowa masa (Qur’ani)….”

(41 / ﻓﺼﻠﺖ 42/ ).

Wannan ayar ta kara tabbatar mana da cewa babu yadda wani zai iya jirkita Qur’ani ta hanyar kari ko ragi.

A wata Ayar Allah(swt) yana cewa:

“ﻭﺍﻥ ﻛﻨﺘﻢ ﻓﻲ ﺭﻳﺐ ﻣﻤﺎ ﻧﺰﻟﻨﺎ ﻋﻠﻰ ﻋﺒﺪﻧﺎ ﻓﺄﺗﻮﺍﺑﺴﻮﺭﺓ ﻣﻦ ﻣﺜﻠﻪ”

‏( ﺍﻟﺒﻘﺮﺓ / ٢٣ )

“In kuna shakka akan abinda muka saukarwa bawanmu (Annabi(saw) (Qur’ani); to ku zo da wata sura misalin tasa (Qur’ani)”.

Da Allah(swt) yayiwa Kafirai wannan kulen suka kasa, sai Allah(swt) yace;

“ﻗﻞ ﻟﺌﻦ ﺍﺟﺘﻤﻌﺖ ﺍﻻﻧﺲ ﻭﺍﻟﺠﻦ ﻋﻠﻰ ﺃﻥ ﻳﺄﺗﻮﺍ ﺑﻤﺜﻞ ﻫﺬﺍ ﺍﻟﻘﺮﺁﻥ ﻻ ﻳﺄﺗﻮﻥ ﺑﻤﺜﻠﻪ ﻭﻟﻮ ﻛﺎﻥ ﺑﻌﻀﻬﻢ ﻟﺒﻌﺾ ﻇﻬﻴﺮﺍ ”

‏(ﺍﻹﺳﺮﺍﺀ : 88).

“Ka gaya musu; lallai da Mutane da Al-jannu za su hadu don su kawo irin wannan Qur’anin ba zasu iya kawo irinsa ba; duk taimakekeniyar da zasu yi a tsakaninsu”.

A WADANNAN AYOYIN DA WASU MASU YAWA A QUR’ANI, ALLAH(SWT) YA TABBATAR DA CEWA BABU WANDA YA ISA (MUTUM KO AL-JANI) YA KAWO SURA KO AYA DAYA TAL IRIN TA QUR’ANI.

A shia, duk wani hadisi da ya sabawa ayar Qur’ani; to ba zancen Annabi Muhammad(saw) da Imaman Ahlul-bayt(as) ba ne; ba zai yiwu maganar Allah(swt) da ta Annabi(saw) suyi karo ba. Don haka, duk wata ruwaya da tazo a littafan Shia ko Ahlus-Sunnah game da canzawa ko rashin cikar Qur’ani batacciya ce (bata inganta ba).

➖➖➖➖➖➖➖➖

Abdulrahman Murtala – abdulrahmanyj@gmail.com

🌹🌈🌹🌈🌹🌈🌹🌈🌹

Share with your friends
  •  
  •  
  •  
  •  
  •  
  •  
  •  
  •  
194 views

Leave a Reply

Be the First to Comment!

avatar