KUKAN KURCIYA

By Dauda Haruna.

“*Ina fatan abinda zan fada a yanzun zai canza zuciyar koda mutum biyu ce. Saboda ya canza tunani na gabaki daya.*

*Na raina naira dari (#100). Ina ganin me zan siya da ita. Sai jiya danaje kasuwa naga wani tsoho yana siyar da yalo. Kallo daya zakai masa kasan yayi yawo harya godema Allah.*

*Gabaki daya yalon bazai wuce na naira dari biyar ba. Na dauki #100 dani na raina na bashi. Tsohone da zaikai shekaru 70. Hawaye ne cike da idanuwanshi lokacin da yake mun godiya.*

*Abin ya dame ni sosai da sosai. Maganata anan itace. Abinda ka raina zai iya canza rayuwar wani ta yini daya. Suna nan gefen hanya. Masu saida yalo, abin tsifar kai, igiyar guga, shebir, masu kasa yar albasa da bata wuce kudin powder din da wasun mu ke shafawa ba.*

*Mu daina dauka yayi kadan. Naira ashirin in kuka bayar yan uwa zata zama mai ma’ana a awa daya na rayuwar wani. Ku fara daga yau.*

*Karku jira ku samu da yawa kamun ku bayar. Karku jira ranar da baku da tabbas din zuwanta. Kuyi amfani da ranar da kuka gani ku bayyana murmushi a fuskar wani bawan Allah.*

*Abinda ka raina shi wani yake nema rayuwarshi ta canza ta rana daya. Dan Allah ku duba. Kuyi ko sau daya. Ku tura gaba wani yagani. In ba zaka iya canzawa da bayarwa ba ka tura sakon yaje gaba.*

*In wani ya karanta ya aikata zai zama kana da kaso a ciki. Allah ya bamu mu taimaka. Allah ya horema al’ummar shi (Amin thumma amin)*

*Nagode da lokacin ku.*”

Share with your friends
  •  
  •  
  •  
  •  
  •  
  •  
  •  
  •  
152 views

Leave a Reply

Be the First to Comment!

avatar