BUHARI: ZIYARAR AIKI KO SHAKATAWAR IYALI?

Daga Audu Bulama Bukarti

Sanarwa ta gabata cewa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai tafi kasar Turkiyya tare da Shugaban Kwastam na kasa Kanal Hameed Ali domin tattaunawa akan shigo da makamai zuwa Nijeriya ba bisa ka’ida ba. Amma sai ga hoton sa tare da matarsa Aisha Buhari da dansa Yusif Muhammadu Buhari da kuma ‘yarsa Halima Muhammadu Buhari cikin jirgin shugaban kasa suna shakatawa akan hanyar zuwa Turkiyya.

A lokacin da Aisha Buhari ta kwashi wakilai 21 zuwa taron majalisar dinkin duniya a kasar Amurka. Na yi magana an ce attajira ce ita ta dauki nauyin komai. Amma attajira ce mijinta ya nemi taimakon kudaden talakawa domin sayen tikitin takara?

Yanzu wannan tafiyar ta aiki ce ko ta shakatawar Iyali? Shin da kudin talakawan da ba sa iya cin abinci sau uku a rana za a yi tafiyar shakatawar iyali? Shin sunayen Iyalin shugaban kasa na jikin kuri’ar zabe lokacin da aka zabe ka?

Yallabai idan irin rayuwar Trump kake so ka rika yi mukamai za ka ba su cikin Gwamnatinka kamar yadda ya yi. Don haka sai mu san da wa muke mu’amala.

Share with your friends
  •  
  •  
  •  
  •  
  •  
  •  
  •  
  •  
69 views

Leave a Reply

Be the First to Comment!

avatar