TARIHI DA WAKOKIN ALHAJI (Dr) MAMMAN SHATA KATSINA


Bilkin Sambo ta Mamman Shata!

Ana yi wa Dr Mamman Shata kirari da

"Sarkin wakar Kanawa, Duna na Bilkin Sambo.
Warga-wargan namiji
Mai daci kamar guna…"

Wai shin Bilkin Sambo, matar sa
ce, ko kuma k'anwar sa ce? Kuma
meye tsakanin su da Yalwa?

Wannan ita ce tambayar da
Fatuhu ya yi a Majalisar
Marubuta kwanan nan. Ni kuma
na ba shi amsa kamar haka:

Malam Fatuhu,
Lallai ka yi tambaya ga d'an gida.
Tambayoyin ka su ne:

1. Wai shin Bilkin Sambo, matar
Shata ce, ko kuma k'anwar sa
ce?

2. Kuma meye tsakanin su da
Yalwa?

BILKIN SAMBO
Wata mata ce a garin Funtuwa,
Jihar Katsina, wato garin da
Shata ya yi rayuwar sa, inda
iyalin sa su ke. A farkon zuwan
Shata Funtuwa, bayan ya taso
daga Bakori (wanda shi ma gari
ne kusa da Funtuwa) sai su ka
shak'u da Alhaji Nagoya, wani
d'an kasuwa mai cinikin auduga.
Nagoya ya d'auki Shata kamar
d'an sa. Don haka ne ya had'a shi
da wasu 'ya'yan sa biyu mata,
Indon Dutsen Reme da k'anwarta Bilki.

Akwai kuma Sambo, wanda shi ne
babban d'an Nagoya d'in. San da
duk aka yi haihuwa a gidan Alhaji
Nagoya, ya kan kirawo Shata ya
ce, "Ga uwargida!" ko "ga
ubangida na yi maka!"

Da aka haifi Bilki, Shata ya na makad'in
gidan, sai maigidan ya ce masa,
"To ga sabuwar uwargida na yi
maka."

Daga nan ne ita Bilki,
wadda akan kira Bilkin Sambo, ta
zama Bilkin Shata, sa'annan shi
ma Shata ana ce masa Na-Bilkin
Sambo (har marokan sa su kan yi
masa kirari da "Mai tambura Na-
Bilkin Sambo!").

Abin mamaki, Shata bai yi Bilki
waka ba (a iya sani na), amma
kuma ya wak'e Indo da wakar
"Indon Dutsen Reme Lambawan."

A yanzu ita Indo ta na auren
Magajin Garin Musawa, Alhaji
Abdullahi Inde. Ita kuma Hajiya
Bilki, ta nan da ran ta a
Funtuwa, inda ta yi aure har ta
hayayyafa. Ga hoton ta nan
tare da d'an ta (amma tsohon
hoto ne, domin na ke jin kila ma
wannan yaron ya girme ka!)

2. YALWA
Akwai Yalwa guda biyu a rayuwar
Shata. Ta farkon ita ce kanwar
sa mai bi masa, wadda ta rasu
tun tuni. A garin su Musawa ta
yi aure, har ta haifi d'a wanda
ake kira Umbaje (ka san ana yi
wa Shata kirari ana cewa "Uban
Umbaje").

Yalwa ta biyu kuma ita ce Hajiya
Yalwa Bature, wadda matar sa
ce da ya fi so a rayuwar sa. Sun
dad'e da rabuwa, har ta auri
marok'in sa Alhaji Bature Sarkin
Magana (wanda shi ma ya dad'e
da rasuwa, tun kafin Shata ya
rasu). Hajiya Yalwa ta na nan
zaune a Kaduna tare da 'ya'yan
ta, cikin su har da 'ya'yan da su
ka haifa da Shata (Umma, matar
Kanar Bala Mande wanda ya
tab'a yin gwamna a zamanin
Abacha, kuma ya yi ministan
Obasanjo), da Bilkisu Shata
wadda d'aliba ce a fagen Political
Science a Jami'ar Abuja, da
kuma Nura).

Da ka ji ana kiran Shata, "Shata
na Yalwa", to k'anwar sa din nan
ake nufi, ba matar ba, domin tun
kafin ya auri Yalwa ake ce masa
hakan.

Allahu akbar! Allah yayi mata rasuwa yau laraba 23/01/13

Allah yajikanta ya gafata mata yasa aljannace makomarta ameen.

Da fatan ka gamsu. DAGA BAHAUSHE MAI BAN HAUSHI-IBRAHIM SHEME- MAR. 2007


WAKAR SHATA DA TARIHIN ABBA SIRI-SIRI
-Hamisu Adamu Gamarali Funtua
-Munayya A Mahmoud

"Shekara arba’in da biyar Abba yai cikin aiki,
Shekara ashirin da biyar Abba na ciki N.A,
Shekara ashirin daidai Abba yai cikin gwammen,

Shekara ashirin da biyar Abba yai cikin N.A,
Aikinshi biyar kowane shekara biyar Abba;
Yayi malamin daji,
shekara biyar Abba,
yayi malamin hanya,
shekara biyar Abba,
yai zama cikin yadi,
shekara biyar Abba,
yai zama cikin ofis,
shekara biyar Abba biyar ya riki LPO,
Abba biyar ya riki LPO,

Shekara ashirin daidai Abba na cikin N.A,
Aiki hudu yai kowane shekara biyar Abba;
Yayi siniya sabis,
shekara biyar Abba,
kuma ya zama A.D.O,
shekara biyar Abba,
kuma ya zama ful D.O,
shekara biyar Abba, biyar ya riki A. rector,

ka bari haka nan Abba,
mutum tara yake Abba,
kai ka tuna bashi cika goma,
hum, hum ban Allah,
Cha mutumin kirki”

Cikakken sunan wanda aka yima wakar shine Alhaji Muhammadu Sani Abdulkadir wanda aka fi sani da Abba 33, an haifeshi a cikin birnin Katsina a wata unguwa da ake kira ‘Yantaba, shiyasa ma Shata ke cewa “shi Abba ko cikin birni unguwarsu ‘yantaba… amma fa baya shan taba… dottijo sai tuwon shi mai nama… sai wata ‘yar furarshi mai nono”

Yayi zama a garin Funtua tun zamanin N.A wato (Native Authority) yayi wasu ayyuka daga bisani ya shiga soja “ka bari haka nan dutse… mutum tara yake Abba… kai katuna bashi cika goma”

Abba 33 mutum ne mai son huldar jama’a da taimakon adini, ya assasa masallatai da dama a ciki da wajen garin Funtua tare da yunkurin gina wani a Tafoki Road Filin Kwallo Funtua amma Allah bai nufa ba, ya kuma kawo abubuwan cigaba da dama a garin Funtua daga ciki akwai asibiti na farko farko mai zaman kansa a Funtua wato KHAMEC da gidan man TATICO dake Jabire Funtua “Tab! Mutumin kirki”

Allahu akbar!!! Allah ya karbi ran Abba 33 a ranar asabar 01/12/1984 daga cikin fitattun ‘yan’uwansa masu kishin Funtua akwai Sa’in Katsina Alhaji Amadu Na Funtua da Marigayi Alhaji Iro Bukadi da Marigayi Sarkin Sudan Na Katsina Alhaji Dr Garba ja Abdulkadir Allah yajikansu da rahama, ya sanya aljanna ce makomarsu, ya kuma albarkaci zuriarsu baki daya amen, shi kuma Sa’i Allah ya kara masa da lafiya da tsawoncin kwana ameen.

"Lambar "33" Ta samo asali ne daga lambarsa ta shiga makarantar Secondry. So a komai nasa daga books dinsa, zuwa duk wasu kayansa na makaranta, sai yake rubuta 33. Abun hawansa na farko (KEKE) sai ya rubuta masa lambar 33 da kansa. Hakan ne yasa class mates da abokansa suka yi masa lak'abi da Abba 33. Da Allah ya buda masa, ya daukaka shi, har lambar motocinsa ma sai yake sa 33. Yanzu haka dukkannin yan gidan mu, mu goma sha takwas duk Allah ya hore mana motoci gabadayan mu maza da mata. Kuma duk wannan lamba 33, ita muke amfani da ita, har ma matan da y'an mazan gidan mu suke aure, duk wannan dai 33 ita muke amfani da ita. Mun sha siyen lamba da tsada, kawai don mu mallaki lambar 33. So please a daina yi masa wani mummunan zato. Shi tasa ta kare, kuma muna yi masa kyakkyawan zato. Wasu basu san yanda zasu k'are ba.

References
-Hamisu Adamu Gamarali Funtua
-Munayya A. Mahmoud

Share with your friends
  •  
  •  
  •  
  •  
  •  
  •  
  •  
  •  
125 views

2
Leave a Reply

avatar
2 Comment threads
0 Thread replies
0 Followers
 
Most reacted comment
Hottest comment thread
0 Comment authors
anonymousDANBUZU Recent comment authors
newest oldest most voted
DANBUZU
Guest
DANBUZU

Wasiyya Sipikiyya Ta'ala ina rokonka ranar da zan cikaKasa in cika Allah cikin daki naGaban duk iyali na da 'ya'ya da 'yan'uwaAllah ina rokon ka sai a gidanaIdan na cika yan'uwa na gaya mukuDa kun ji cikawata ku taru gidanaIdan har da rana abin yazo ko cikin dareBatun jinkiri kar dai ya faru wurinaIdan anyi sallah an gama kar a dakataA dauka kawai hanyar zuwa kabarinaIdan anka je da zuwa a sani ciki kawaiCikin hankali domin tuno lamarinaKasar kabarin kuma kar a ware daban-dabanA turo gaba daya duk ta watsu a kainaIdan aka kare gini da an tashi an gamaKu koma wajen harkarku ya jama'ataBatun sadakar Uku, ko Bakwai, ko ta Arba'inKaza shekara wallahi babu ruwanaIrin masu kukan nan da ihu da razanaDon Allah na roke ku kar kuyi kainaIna tausayin ku kwarai zuwa gun jana'izaKaza wahalar tafiya hakan kabarinaKaza wahalar wanka da dauko ni don zuwaCikin makara tafiya zuwa karshe naHakika a rannan da da ikon da zan iyaYa sa tausayin a wajen dukan jama'anaAnan zan tsaya domin wasiyarmu ta tsayaMudi Spikin ne uba ga Amina

anonymous
Guest
anonymous

Anonymous writes:Allah kasa ya huta ka sanya aljannah ta zama makoma ameen Ya Allah.