Mafarkin Danbuzu — DANBUZU

Ina dan kishingide ina kurbar sassanyan ruwa, ga kumawata irin gara a gabana, wacce maidakin tawa ta shirya mani, kasan sabuwar amrya ce, amma ta dara sauran amare. Kai bari dai nayi maku irin ta mahaukaci; a taikace dai, duk duniyarna ta Maliki-yaumiddini, babu macen da ta iya girki kamar maidakin tawa!!! …

Da la´asariyya sakaliya ta wata ranar Asibicin watan jiya, na dawo daga Katsina ina daf da shiga garinmu — Musawa, kawai sai na tuna da dansaurayin akuna dake debe mani kewa, wato Buzu. Sunasa kenan kuma kar kayi tambaya akai!
Bayan na shiga cikin gida, kuma maidakina tayi mani hidindimun tarya kamar yadda ta saba mani idan na komo daga wani waje, sai na dakko jakata na bude na dakko wata farar leda wadda aka zazzaneta da jan rubutu, na gabatarwa maidakin tawa a matsayin tsarabarsu ita da Buzu, na kuma shaida mata cewa nayi mai takanas-ta-Kano ne na biyo ta Maciyar nama ta Yahuza Suya ne dominsu, sai tayi godiya ainun, sannan ta fuskanci abin da ke kunshen — shiryayyen naman kaza da nasa, hanta, koda, kundu da kuma masa, baya ga ababen shaye-shaye.
Ina dan kishingide ina kurbar sassanyan ruwa, ga kumawata irin gara a gabana, wacce maidakin tawa ta shirya mani, kasan sabuwar amrya ce, amma ta dara sauran amare. Kai bari dai nayi maku irin ta mahaukaci; a taikace dai, duk duniyarna ta Maliki-yaumiddini, babu macen da ta iya girki kamar maidakin tawa!!!
´Yaya! Yaya!! Yaya!!!´ maidakina ta kirani cikin kuwwa, ´lafiya?´ na tambayeta cikin hanzari yayin da nayi firgigi na mike tsaye tare da tunkaro dakin aku, domin nayi imanin daga can ne take yi mani wannan irin kira, wanda kuma ya tabbatar mani ba lafiya ba.
Shidai wannan aku dake karkashin ikona dangatane, domin kuwa ko a cikin gida dakinsa guda aka ware mashi yayi ta harkarshi ba mai saka mashi idanu, ga kuma tagogi da fankarsa, don haka ba ruwansa da zafi. Bugu da kari, cima sai irin wacce yake so; nama tayi mashi cari akan nama da yaki yake ci, wai shi Allah ya sauwake yaci naman dangoginsa, wai idan inaso yaci sai dai muyi da wajewa: in fara cin naman nawa jinsin to shima sai yaci na nasa jinsin, ko kuma in kawo mashi nama dan´adam. Amma baya ga wannan, ababen da Buzu bai ci bawai sun taka kara sun karya bane.
Koda na isa dakin Buzun, sai na iske mai sunan wani mawaki — Hassan Wayam. Ni ko kawai sai na saki baki nama kasa cewa komi. Da farko na zaci baki suka hada shi da maidakin tawa su zolaye ni, amma daga bisani nayi amfani da bayanan da maidakin tawa ta bani, sai na fuskanci itama bata da masaniyar inda Buzun ya falla. Amma dai, kalaminta guda da nayi ta jinjinawa shine: wai ita da shi su dan sami sabani da safe wajen karin kumallo, amma daga bisani sun daidaita. Don ko a dazu da wata bakuwar yarinya wacce aka aiko na manta bata ja kofar gidan ta rufeta ta baya ba, har awaki suka shigo za suyi barna shi ya koresu, kuma ya isketa har daki ya shaida mata, sannan ita kuma taje ta bame kofar gidan.
Kasan ance idan rakuminka ya bace, to ka nemeshi har cikin tandun kwalli, to nidai har a kafar allura na nemi aku, amma Allah bai sa na dace da samunsa ba. Haka dai na hakura na dangana, na kuma maida komai ga Allah.
Bayan na komo bigiren da maidakinata jera mani ababen ciye-ciye, lashe-lashe da shaye-shaye, kuma na himmatu da aikatasu, sai hakan taki yiwuwa a sabili da wasikar jaki dana bige da karantawa. Na dai na zame bisa darduma sai barci, nan kuma ga gara iri-iri a gabana.

* * * * * *

Al´amrin Buzu kuwa, tuni har ya kai Dayi. Wai ashe da safe bayan nayi sammako na tafi Katsina, sai ita maidakina tai komarwar barci abinta, tunda dama ranar Asabarce kowa yana gida yana hutawa. To lokacin da ta tashi daga barcin domin ta shirya kayan kalaci ya dan saba da lokacin da muka saba. Don haka koda aka kaiwa Buzu nasa kalacin sai yaki kallonsa, kuma yace kodai ai mashi cikakken bayani akan lattin kawo mashi kalaci da akayi ko kuma yayi yajin cin abinci kenan daga nan har illa masha´Allahu. Bugu da kari, kuma wai shi yasan hakki da ´yancin kansa.
To wai itamaidakina abinda yafi batahaushi a duk kalamansa shine: wai ya tsuntsu zai ce mata yasan ´yancinsa, kuma har yake ikirarin zai yajin cin abincin. A cikn wannan yana yin batasan lokacin da tace mashi aku kuturun wofi ba. Kuma ta kara da cewa ko ya karya koma kar ya karya duka uwarsu daya ubansu daya. kuma idan ya kara magana nan wurin to zata sa yara su yanka mata shi tayi farfesunsa. Kuma banda an sakarwa tsuntsu fuska, taya har zai dinga irin wannan kalaman ga bil´adama da cikin jejisa yake wajen da wanda yafika karfi zai kamaka ya cinye ai da bai ce haka ba. Nan dai t gama ´yan fadace fadacenta tai tafiyarta dakinta ta bashi guri.
To wai ashe shi duk a cikin maganganunta, magana daya ce ta bashi haushi; lokacin da tace masa ´aku kuturun wofi´. Shi kuma yaga ta yaya zai zauna a cikin bil´adama har suke ci mashi fuska haka. Don haka ya yanke shawar yayi komawarsa daji, ammafa bayan ya gama karade daukacin nahiyoyi da biranen ´yan´adam, ya gansu ido-da-ido kamar yadda yake ganin ta akwati talabijin a kafafen yada labarai na gida da na waje. Cikin har da guraren da ake yake-yake.
A lokacin da ya yanke shawarar hakan,da farko ya yardarwa kansa cewa idan Mako ya kewayone zai yi hijirar, amma daga baya ya yanke shawarar bari yayi tafiyarsa yanzu kawai; domin kuwa idan ya bari sai Makon ya dawo, to zai iya hakura. Kuma idanfa ya hakuran shikenanfa an sha shi basulla.

Share with your friends
  •  
  •  
  •  
  •  
  •  
  •  
  •  
  •  
Tags: ,
48 views

Leave a Reply

3 Comments on "Mafarkin Danbuzu — DANBUZU"

avatar
Sort by:   newest | oldest | most voted
sultanselim
Guest
وَنَجِّنَا بِرَحْمَتِكَ مِنَ الْقَوْمِ الْكَافِرِينَhttp://www.islamicity.com/MOSQUE/ARABICSCRIPT/AYAT/12/12_86.htmBu Yazılanlar Hayatımından Kesitler Okurken Herkes Kendi Hayatının Kesitlerini Tekrar Gözden Geçirme Ve Böylelikle Nerden Nereye Nasıl Bir Yol Aldığımızı Birlikte Görebilmek İçindi…Ve Herkes Şunu Bilmeli ki Kulluğumun İfadesinde Hala Bulunabilmiş Değilim Hayretler İçinde Kalmış Aciz Bir Kul Olmanın Dışında…Tek bu sayfa ciltler dolusu kitabı özetemeye yeter…in the name of ALLAH the most beneficent the most mercifulnone has the right to be worshiped but ALLAH and Mohammed is the messenger of ALLAHidentity muslimname: muslimsurname: the muslimsfathers name:the adammothers name: evebirthplace:citizen of the worldthe profession:the path of ALLAHreligious sect:mohammed of a religious ordertemperament : coterie brotherhoodnationality:hanif'phylo-:humancountry:the place to the master of ALLAHthe target:for ALLAHs sakehanif^'ure islamic monotheism(worshiping ALLAH alone and nothing else).الصلاة و السلام عليك يا حبيبي يا رسول الله – الصلاة و السلام عليك يا حبيبي يا حبيب الله – الصلاة و السلام عليك يا خيرة خلق الله – الصلاة و السلام عليك يا من بعثت رحمة للعالمين – الصلاة و السلام عليك و على آلك و أصحابك أجمعين – صلى الله عليك و الحمد لله رب العالمينAssalam AlaikumWarahmatullahi Wabrakatuhu!لاَّ إِلَهَ إِلاَّ الله مُحَمَّدً رَّسُوْلُ اللهِصلى الله عليه وسلمLaa ilaaha illa Allaah, Muhammad ur RasooluLlah!There is NO ONE WORTHY of WORSHIP except ALLAAH;Muhammad (Peace be upon… Read more »
DANBUZU
Guest

Is this compatible with the post :confused:

sultanselim
Guest

Not to be You, toothis worlds for peoplea dream like to be endlessa real is similar without endthat known peopleif the worlds immortal(it was going to mortal)that people is mortalthe world!you known to diethe world is spinningnot to be you too …by natlusmiles___████__████_███___▄▓▓▒▒░░▒▓__███____████__████▓███▓▓▒▒░░▒▓__███_███___██__██▒░▓███▓▓▒▒░░▒▓__███__███████▒▒▓█▒░▓███▓▓▓▓░░▒▓___███_████████_██▓████▓▓▓▓▒░░▒▓███_██_███████__████▒▓███▓▓▒░░▒▓__██████_____████████▓█████▓▒▒▒██▓___███████__█████████▒▒███▓▓▒██▓▓▒▓______████ _██░░▒▒▒▒▒▒░▒██▓██▓▓▒░▒▓__█___________██░░▒▒░░░▒▓████▓▓▒░▒▓__██_________█░░░░▒▓▓███▓▓▒▒░░░▒▓_████_________█▒░░▒▒▓▓███▓▓▒░░░░░▒▓__█████_______█▓▓▒▒▓▓▓███▓▓▓▓▒░░▒▓___█████_______███▓▓▓▓███▓▓▓▒▒░▒▓____████______███████▓▓▓▒▒▒░░▒▓_________█______████▓▓▓▒▒░░░░▒▓_____███_█_█__█▓▓██▓▓▒▒░░▒░▒▓____█████__█_█░░▒▒▓█▓▒▒▒░▒▓___██████___█_____█████____████____█___███_█████_____██____█__██____██████______█___█_██_______████_________███__________██_________██____________█_________█________█________█________█ Ruby in Rose'syeşimyıllarca kaybolmuştum bir soranım çıkmadıyaralı kalibimi saracak bir-gül şifam olmadıen çok özlediğim can bir hatrım sormadıekmeğimi bölüşecek bir tas çorbam olmadışekilden şekile kırk boya bir işe yaramadışu gülen yüzlerden bir çift gözüm olmadıiki elim çarmıktan bir an kurtulmadıikinci bir canan bir canım hiç olmadımutluluk çiçeğim bir bir yaşlandıkça solmadımaziye gömdügüm her an bir damla kan olmadıby natlusmileshttp://selim-sultan.blogspot.com/http://tefekkurvesukur.blogspot.com/