Hafizin Aljan — Danbuzu

A unguwar PRP dake yankin Gama a birnin Kano, akwai wata makarantar hardar Alkur´ani ana kiranta Madarasatu Miftahul Kur´an. Wata rana, wata daga cikin dalibai na zaune ana ta karatu, kawai sai ta fara nuna wata halayya wadda ga dukkan alamu ba yin kanta bane. Don haka sai hukumar makarantar ta yanke shawarar yiwa wannan daliba karatun fatattakar aljan daga jikin bil´adama, wato rukiyya. …

Wani malami da ake kira Malam Jamilu shine ya bude rukiyyar da fara rera karatun akan wannan daliba mai suna Ummi. Malam Jamilu ya ci gaba da karatu irin na rukiyya, yashiga Kur´ani ta nan , ya fita ta can, ya bulla ta Idhawaqa, ya kurdo ta tabara, ya ratsa Kuluhiya. haka dai Malam Jamilu ya ci gaba harma ya fara yanko wurare masu zafi daga can sama. Da aljanin dake bisa Ummi ya ga abin ya fara wuce gona da iri, sai kawai ya cane suka ci gaba da rera karatu tare da Malam Jamilu, da yake shima aljanin mahaddacine. Koda Malam Jamilu ya ga haka sai ya hasala, ya kara zabura wajen kurdawa cikin Kur´ani; koda aljanin nan ya fuskanci abin dake faruwa sai ya ma kara daga murya da fitar da ka´idojin tajwidi, harda bayyana kalkala da baiwa maddoji hakkinsu. Da Malam Jamilu ya ankara, sai ya nemi sulhu ta hanyar dakatar da karatun da tattaunawa da aljanin domin sasantawa. A cikin tattaunawar ne ma Malamin ke tambayar aljanin ko a ina suka gamu da Ummi har ya samu ya shiga jikinta. sai aljanin ya bayyana mashi cewa ai a makarantar bokonsu ne, wato Makarantar Sakandare ta Darussan Addini Musulunci dake Gama Tudu. Kuma ya shiga jikinta ne domin ramuwar gayya. Koda Malamin ya tambayi wannan aljan ko lafin me Ummi ta yi mashi, sai ya kada baki yace, ¨Wai tashiga bandaki ne a guje, har ta taka mani da, yanzu hakama dan nawa na nan kwance yana jiyya; kuma na sha alwashin bazan fita ba har sai ya warke¨. Can daga gefe kawai sai wani Malami da ake kira Malam Muhammadu ya fara fada har da daga murya,wai ya za´asakarwa aljani fuska harma a ke saurararsa; don me ba za´a ci gaba da karanto surori da ayoyi masu zafi ba. To bari shi ya zo ya yi karatun, kuma idan ya fara bai tsayawa har sai aljanin ya kone kurmus. Koda aljani yaji haka sai ya fusata, yace, idan dai Malam Muhammadu bai zo ya karbi rukiyar ba, to bai kaunar Allah. kuma wai da me yake takama ma, ba da karatu ba? To ai shima hafizine mahaddacin Kur´ani, mahaifinshi babban Malami ne a cikin aljanu. Kuma idan Malam Muhammadu yana da ja, to yazo ai zubeben kwarya. Aljanin ya kara da cewa, kai shifa ya san ya fa ma girmi Malam Muhammadu a hardar Kur´anin, domin ya san hardarsa tafi tashi kwari nesa ba kusa ba; don haka ya shiga taitayinsa.
Nan dai Malamin yai lakwas yaci gaba da zazzare idanu kamar ance kyat! ya ruga. Daga karshe dai an sami shawo kan wannan aljani cikin ruwan sanyita hanyar yi mashi nasiha a matsayinshi na aljani musullmi kuma mai ilmi.
Bayan faruwar wannan balahira ne ma, anzo ana mayarda yadda akayi a majalisar marasa aikin yi da mukan zauna muyi musun kwallon kafa da sauransu; shine ma har ake bada labarin yadda wani aljani sukai da mai rukiyya. Wai da mai rukiyyar yai karatu yai karatu sai aljanin yace zaifita amma sai mai rukiyyar ya amince da sharadi guda. koda mai rukiyyar ya tambayi aljanin ko wane sharadI ne wannan, sai ya kada baki yace, ai ba wani mai wuya ba ne face kawai idan ya fita daga kan marar lafiyar, to zai komo kan mai rukiyyar. Sai mai rukiyyar yai firgigi yace, ai kawai aljanin yai zamansa anan ba sai ya fito ba. Nan ya tashi da sauri ya kara gaba yana fadin Allah ya rufa mashi asiri, kuma in Allah ya yarda daga yau bazai kara cire aljanba, kuma koda jikin uwarsa ya shiga. To Allah yasa mu dace, amin summa amin.

Share with your friends
  •  
  •  
  •  
  •  
  •  
  •  
  •  
  •  
104 views

8
Leave a Reply

avatar
8 Comment threads
0 Thread replies
0 Followers
 
Most reacted comment
Hottest comment thread
0 Comment authors
bgsbnuraddeenmmkassimdandagoFaisalbaristaDANBUZU Recent comment authors
newest oldest most voted
Sulemanmada
Guest
Sulemanmada

Na ji dadin wannan takaicaccen labarin naka

DANBUZU
Guest
DANBUZU

Da fatan dai ka koyi wani darasi a ciki?

Sulemanmada
Guest
Sulemanmada

Insha Allah!

Faisalbarista
Guest
Faisalbarista

Gaskiya naji dadin wannan labarin kuma allah ya kara tsaremu ameen.

kassimdandago
Guest
kassimdandago

Yanzu nake jin labarin nan. Kai a ganinka. Yaya za a yi wa aljan in ya shiga jikin mutum, karatu ko nasiha?

nuraddeenmm
Guest
nuraddeenmm

Amma mallam yaji kunya wallahi

nuraddeenmm
Guest
nuraddeenmm

Amma mallam yaji kunya wallahi

bgsb
Guest
bgsb

Allah ya sa mudace.