Spirit: Magani ko Aljan? — DANBUZU

A kwana-kwanan nan ba da dadewaba ana gobe zan dawo Musawa daga Calabar, wata baiwar Allah mai suna Ekaite dake zaune anan unguwar Bogobiri tayi wani abu shi ba abin haushiba ba kuma na dariya ba.In dai takaice maku labari, a wata ranar Asabar ne bayan an gama wani bikin binne gawa a nan unguwar, dare yayi kowa ya tafi ya kwanta, kawai sai ta tsiri aske duk wani gashi dake duk wani loko a jikinta. watakila saboda shagalin bikinta da za'a tashi da shi washe gari Lahadi a cocin Presbetariya. …

Bayan ta gama da abinda ya shafi hammata da sauransu, ta shagala da aske gashin mara, kuma ga barci yana neman danneta asabili da gajiyar zurga-zurgar da ta wuni yi, ba tare da tayi auneba kawai sai taji wani abu zuuu! har tsakiyar kanta gami da radadi daga kasan mararta, dubawar da zatayi haka, sai taga jini yanata kwarara, ashe yankewa tayi a gefen clitoris dinta a garin kwakulo gashi ta aske. "O! my God I don destroy am," kalmar da ta furta kenan cikin rudewa. kawai sai ta tashi tayi daka a guje tare da fadin "Thank you God". Hakan ta faru ne bayan ta tuna wajen da mahaifinta ke ajiye kwalaben magani, da yake ma'aikacin jinyane. Kash! rashin tabbas na NEPA sai kawai suka dauke wuta bayan ta riga ta dakko spirit ta kuma antayashi, harma yayi ambaliya cikin wajen da yafi ko ina tsada ajikinta ba tare da ta saniba saboda rudewa. Shigar spirit gurinda bai kamata ya shigaba yasa radadi da zugin sukama ci uban nada, ga kuma duhunda NEPA ta haddasa. Sai kawai ta ruga dakin girki cikin dimauta domin dakko ashana. Dakkowarta keda wuya sai ta kyasta domin ta haska wajen don ganin me ke faruwa. Kasan spirit kamar fetur yake, kanga ashanar keda wuya, ji kake 'butt!!!' gobara ta tashi a wajen. Ekaite kuma a iya saninta ruwan spirit dinnan da ta sanya shine ya haddasa gobarar, saboda haka bata san lokacinda ta fara ihu tana fadin "spirit! spirit!! spirit!!!" ba, su kuwa mutanen gida tare da jama'ar gari da suka ji ana fadin spirit cikin ihu da kuka, kuma gashi 'yan sa'o'i kalilan bayane akayi bikin binne gawa tareda 'yan tsafe-tsafe sai suka zaci spirit da take ambata na Aljan ne ba na maganiba. Saboda haka ba wanda ya ko leko don tsoro. Nan dai wannan waje ya kone kurmus, aurenda bai yiwu washe gari kenan ba. Na dai dawo Musawa na barota a gadon Asibitin Koyarwa na Jami'ar Calabar. Don ko da naje dubiya na iske ta bajeshi wani likita na shafeshi da wani magani mai maiko sai kyalli yake, gashi kuma yayi wani irin launi tamkar jikin jakin dawa. Don ko kallo na biyu ban iya na sake yi masa ba, domin ya riga ya gama konewa, ya cakalkale ya kwabe tamkar gwalagwajen tumatir. Daga baya ne ma ina gida nake samun labarin wai mijin ya fasa, wai bai son konanniyar haja, wai ya nakasa, launinsa da… sun sauya. To! Allah ya kyauta. Amin suma amin.

GA MAI BUKATAR KARANTA IRE-IREN WANNAN LABARIN, YA TAFI CAN KASAN WANNAN BLOG, SUNA NAN BIRJIK: 😆

Share with your friends
  •  
  •  
  •  
  •  
  •  
  •  
  •  
  •  
96 views

Leave a Reply

8 Comments on "Spirit: Magani ko Aljan? — DANBUZU"

avatar
Sort by:   newest | oldest | most voted
Sulemanmada
Guest

Matar ba ta da hankali

DANBUZU
Guest

Ko?!

Faisalbarista
Guest

Gaskiya mijin ya taimaka mata

DANBUZU
Guest

Anya :confused:

Garbasule
Guest

Danbuzu ka bani dariya, yaushe zaka rakani nima na dubo ta.

Abdallah200
Guest

Nima aje dani

DANBUZU
Guest

Kar ku damu!

alarammah
Guest

Gaskiya danbuzu baka yi dede ba, me yasa ka gudo? ai da sai ka tsaya ko zasu baka ita SADAKA…. lol